BAKIN GANGA 3to8

​[3/31, 5:39 PM] -Roshni: 20/03/2017
BAKIN GANGA
 BY
Mamu

 &

Sanam
               <<<<<4>>>>>>

Bayan ta gama aikin duk da take, sannan ta samu tayi wanka tayi sallolinta, tana zaune kan sallaya da tayi sallah ne taji sallamar Abbanta, tayi sauri ta tashi ta fito, don ta gaida shi.

     “Abba sannu da zuwa”

 Ya amsa da

 “Yawwa Hamida yar albarka, ince dai komai k’alau?”

Tace 

 “Lafiya k’alau Abba ”

Yace 

“To madallah Hamida Allah ya taimaka.”

 Ta tashi ta koma d’akinsu.
*

Hanyar komawa garinsu ya kama, tafiya yake da gudun tsiya, kamar baya son rayuwarshi, sauri kawai yake yaga ya isa Sokoto, ga duhu ya sauka, yasan yanzu hankalin Mamie a tashe yake, ganin har yanzu bai k’arasa ba, ga kuma wayoyin shi duk ba charge a mace suke.

    Koda ya iso gida kusan 10 na dare, side d’inshi ya fara shiga yayi wanka, sannan ya shiga cikin gidan.

    Mamie na ganin shi ta sauke wani irin ajiyar zuciya,

  “Ina ka tsaya har dare yayi haka Hudu?”

 Yana k’arasawa wurinta yayi  hugging d’inta, yana murmushi. yace

 “Ina wuni Mamie?

 Ta ansa mishi da

“Lafiya k’alau ya hanya?

Yace 

 “Hanya kalau Mamiena”
    Chuchu dake zaune gefe ta gaida shi ya ansa, Mamie tasa aka kawo mishi abinci ya dan ci kad’an, ya tashi yayi musu saida safe ya wuce side dinshi.
*

  Alhaji Jafar asalin d’an Sokoto ne, wanda yake zaune da iyalinsa matarshi Hajiya Maryam, itama haifaffiyar yar Sokoto ce da yaransu 3 Namiji (Hudu) da ‘yan Mata 2, Rukayya (Ummi) sai k’aramar Balkisu (chuchu) da yake Ummi tayi aure shekara 2 da suka wuce, sai ya rage chuchu kawai ke gidan.
     Familynsu is a renowned family a garin sokoto, Alhaji Jafar ba k’aramin mai kuddi bane, he’s into harakar gine-ginen gidaje yana saidawa, wasu kuma yasa haya, ba abinda iyalinsa suka nema ya kasa musu.
*

 Hudu miskilin mutum ne na k’arshen zance, dalilin haka nema yasa kannensa ba wanda suka shak’u dashi, ko wannensu nesa-nesa yake yi dashi, shidai yaje aiki ya dawo yaga Mamienshi kawai ne aikinsa.
    Bayan dawowar shi side d’insa, d’akinshi ya bud’e ya fad’a kan gadon ya kwanta, ya rufe ido don ya samu ya d’an huta, saboda gajiyar da ya kwaso, kwantawar da yayi memories suka fara dawo mishi na yarinyar da ya watsawa ruwa dazun, sai yanzun yake jin ba dad’i, don kuwa yasan inda wata ce d’an neman rashin mutuncin da zata tafka mishi ba k’arami bane, nan take duk yaji rayuwarshi ta b’aci, yayi daya sanin yin hakan, though yasan bawai da gagan yayi mata hakan ba, amma hak’urin da bai bata bane yasa yake jin ba dadi.
(Mrs)

&

Sanam

[3/31, 5:39 PM] -Roshni: [18/3/2017]
BAKIN GANGA
 By

Mamu

   &

Sanam
****

NOTE: Masu karatu, zaku ga buk ya canja, ya kuma na mutum biyu, dafatar zaku cigaba da binmu.
****

       <<<3>>>

Misalin k’arfe shida na Yamma (6:00pm) Tafe take sanye da uniform na islamiya, da jaka ta rataya a kafad’a mai dogon Hannu, a natse take takonta, ta nufi hanyar gidansu. Da ka ganta kai kasan daga Islamiya ta fito.   

   Tafiya take sauri-sauri kar dare yayi mata a hanya, ga magrib na gabatowa, kawai ji tayi ruwa ya watso mata a jiki, dubawar da zata yi, taga ruwan da suka kwanta a kasan bakin titin layin su ne, wata mota ta fallatso mata a jiki.

     Ta d’aga kai ta kalli motar da ta watso mata ruwan, taga wanda yake cikin motar ya samu wuri yayi parking amma bai fito ba, yayi zaman sa yana shan AC abin shi, bin motar tayi da kallo na d’an lokaci, sannan ta ci gaba da tafiyar da take, ta nufi hanyar gidan su bata ce k’ala ba.

 

Shi kuma ganin hakan da tayi yasa mamaki ya cika shi.

     Shigar ta gidan keda wuya Mama Larai ta hau salati

  “La’ilaha illallahu ni luba yau me zan gani? Hamida yau kuma wasan k’asa kika koma kina yi tsofai-tsofai da girman ki? Kaicho Hamida wallahi Uwarki dai bata yi sa’ar haihuwa ba Hamida.”

     Hamida da tunda mama Larai ta fara magana siraran hawaye ke ta zarya a kumatunta, dama tasan abinda zata tarar kenan.
     ‘Hamida cikakkiyar budurwa wacce bata wuce shekara 23 da haihuwa ba, yar asalin garin gusau ce (zamfara) mahaifiyar ta ta rasu tun tana da shekaru 3 a duniya, bayan rasuwar mahaifiyarta ne, mahaifinta Mal Sale ya k’ara aure inda ya aure Larai yar mak’otansu, wadda tun mahaifiyar Hamida tana raye suke mutunci da ita sosai asali ma la’akari da hakan da Mal Saleh yayi ne yasa ya aurota, domin ta zamo uwa a gun Hamida.

   Sai dai inaa! Larai ta zamo masa k’adangaren bakin tulu, yana gani take musgunawa Hamidar shi daya fi so fiye da komai a rayuwa, amma ba yanda zaiyi.

  Mal saleh Family, zamu iya ce muku they are from a middle class family (Ma’ana su ba masu kuddi ba suba talakawa ba).

    Dai-dai gwargwadon hali yana kwatanta masu. Hamida tana da kanne biyu, domin kuwa Mama Larai ta haifi yara biyu bayan auren su, mace da namiji, Rahma da Imam.

  

  “Mama wallahi ina tafiya ne wani mai mota ya watsa min ruwan dake kwance bakin titi”

   Hamida ta amsata fuska cike da hawaye.

 “To Hamida gani yayi kin masa kama da bola, ba dole ya watsa miki ruwan ba, yo miye marabar ki da bolar ne, ai ni wallahi yamin dai-dai, don wallahi da zan ganshi koda bani da abinda zan bashi zan  masa godiya, had’e da saka mishi albarka, tsinanniyar banza kawai, ni ki wuce zuwa d’ora min abinci kinji ko, azaluma shine ki kai zaman ki wurin yawon iskancin ki don kar muci abinci ko? To wallahi idan zaki kai isha’i baki dawo ba ki sani sai kin dawo kin d’ora shi.” Inna Larai ta idar da fad’anta tana huci, ita a dole an b’ata mata rai.

      Da taga duk bai mata ba, Ta dauko butar da ke gefenta ta jefe Hamida da ita.
(Mrs)

&

Sanam

[3/31, 5:39 PM] -Roshni: 20/03/2017
BAKIN GANGA
By
Maryam Alkali (Mamu)

&

Nafisa Aliyu Musa (Sanam)

   <<<<6>>>>

Ya tashi ya wuce side dinshi ranar ko dinner bai yi ba, yayi salloli ya zauna ya d’auko laptop d’inshi, ya fara aiki har wuraren 11 na dare, baiyi bacci ba.

   Duk bayan mintina takan fad’o mishi a rai, yayi deciding gobe ma ya koma ko zai ganta ya nemi gafararta, da tunani bacci ya dauke shi.
 Safiya ta waye as usual yaje ya gaida su Dady ya wuce office, 12 nayi ya kama hanyar gusau, yau ma kamar jiya haka yayi ta wahalar nema, amma inaa! bai samu wanda ya gane ko bayanin da yake ba, ballantana ya samu wanda ya santa.

     Wuraren 4pm ya kama hanyar dawowa sokoto, a haka sai da ya jera 2 weeks yana zuwa nemanta amma ba nasara, mutanen unguwar har sun kular mishi, ya d’an fara sabawa dasu, bama kamar Mal Bala mai faci, da yake idan Hudu yaje yakan dan yi musu Ihsani.
    Tun baya damuwa har abun ya fara damunshi, wani sa’in ma gani yake kamar ba mutum bace, yana tunanin k’ila Aljana ce, don ko idan ba haka nan ba ya za’ayi ya watsa mata ruwan d’auda (datti) har a fuska kuma bata ce mishi komai ba, ta kama hanya tayi tafiyarta, sannan kuma unguwar da abin ya faru yazo yafi sau 12 amma ace ba wanda ya santa.
*
   ‘Zaune ya sameta akan wani dutsi ta had’a kai da gwiwa tana ta rusa kuka, irin kukan nan mai sosa zuciya, ganinta a wannan wurin cikin wannan yanayi ya k’ara d’aga mishi hankali.
    “Subhanallahi baiwar Allah me kike yi nan ke kad’ai zaune?  kuma kina ta rusa kuka haka?” 

Sam bata d’ago kai ta kalli mai maganarba, sai dai ta d’an tsagaita kukan da take.

     “Ya salam! don girman Allah kiyi hak’uri ki daina kukan nan da kike yi, ta d’ago kai sama ta kalle shi, suna hada ido yaji gabanshi yayi mummunar fad’uwa, ganin cewa yarinyar da yake ta faman nema ce.

  

Nan take ya zube akan gwuiwoyinshi ya had’a hannunshi biyu sama, yace “Don girman Allah ki yafemin, Nine wanda na watsa miki ruwa da mota, tun ranar na kasa sukuni, don Allah ki yafe min.”

     Hamida da tunda ya fara magana ta tsura mishi ido tana kallonshi, ya cigaba da cewa “Don Allah ki yafe lmin ko zan samu natsuwa……….”
 Kiran sallar masallacin gidansu ya tad’a shi, daga mafarkin da yakeyi, yai firgigit ya tashi yana salati, ya zauna yasa hannuwanshi ya rufe fuska yana mamakin abinda ya faru.
 “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un na shiga ukku, yanzu har mafarkin yarinyar nan na farayi” ya zauna yayi shiru na d’an mintuna sannan ya tashi yayi alwala, ya wuce masallaci.

 Chan ya samu Dady, sukayi sallah suka d’auki Al-qur’ani suka fara karatu har sai da haske ya fito, sannan suka shiga gida.

 Daddy ya wuce cikin gida, Hudu kuma ya wuce side dinshi.

 Da yake yau Saturday ba aiki, ya nema wuri kawai ya kwanta yana tunano mafarkin da yayi yau.
By
(Mrs)

&

Sanam

 

[3/31, 5:39 PM] -Roshni: 20/03/2017
BAKIN GANGA 
By
Mamu

  &

Sanam

      <<<<5>>>>

Da tunanin abun kwana (Bacci) ya dauke shi, safiya ta waye ya shirya yaje yin sallama da Mamie, koda yaje Dady ma yana zaune a parlour tare da Mamie, nan ya gaidasu ya tashi ya wuce office.
*
 Hamida kuwa bayan ta idar da sallar asuba ta shiga aikace-aikacen gida, saida ta tsaftace gidan kaf sannan ta d’ora musu zazafen (d’umame) tuwo, ta dama kunu tayi duk abinda tasan ya kamata tayi, sannan ta shiga tayi wanka ta koma d’aki tana jiran masu gidan su tashi, da yake ta gama secondary school kuma Mama Larai ta hana a saka ta jami’a wai aure ya kamata ayi mata, ita bazata iya zama tana had’a  kafada da ita ba, shiko Abba yace bazai mata auren dole ba sai ranar da ta kawo wanda take so sannan zaiyi mata aure.
*

Hudu kam sunan yana office d’inne kawai, amma ga baki d’aya hankalinshi ba’a wurin yake ba, don kuwa har yanzu tunanin yarinyar jiya yake yi. 

       Anya kuwa wannan yarinyar mutum ce? Meyasa batayi mishi rashin mutunci akan abinda ya mata ba? Meyasa ko magana ma baiga tayi mishi ba? Meyasa ta k’yaleshi tayi tafiyar ta?    
 Bayan yana tuna yanda ruwan ya zuba har a fukarta ya kuma b’ata duk kayan dake jikinta, abubuwan dake ta yi masa yawo akai kenan, nan take yaji yana son zuwa Gusau ko Allah zai had’ashi da ita, ya samu ya bata hakuri, ko zai samu sukuni a zuciyarshi. 
    Nan take ya tashi ya kwashi makullan motarsa, ya kama hanyar garin gusau.

    Tafiyar Awa biyu da ‘yan mintina ta kaishi garin gasau. 

     Da  shigarshi bai tsaya ko’ina  ba sai dai-dai wurin da ya watsa mata ruwan jiya, yana tsayawa ya hau tambayar mutane, kowa yace mishi bai gane wadda yake magana ba.

     Yayi ta tambayar mutane amma bai samu wanda ya gane ta ba, a haka har wuraren 5:30 ganin dare na k’arasowa gashi har yanzu bai samu wanda ma ya gane yarinyar ba, yasa ya kama hanya ya komawar shi sokoto.

      7:40pm dai-dai ya iso gida, wurin Dady ya fara zuwa ya gaidashi, sannan ya wuce d’akin Mamie koda yaje ya same ta zaune akan sallaya, ya gaida ita.
  “Hudu ina ka shiga ne yau kayi dare? Ko duk aikin ne yayi yawa?”

 “No wallahi Mamie gusau naje.”

 “Gusau kuma? Ta fad’i cike da mamaki”
     Nan take ya kwashe duk abinda ya faru ya fad’a mata, tayi shiru ta jinjina abin sannan tace

 “Gaskiya baka kyauta ba, amma ba wani abin da zaka tada hankalinka bane, da har zaka kama hanya kaje har gusau neman gafararta, gashi kuma kaje ka k’ona mai da lokacinka a banza, baka samu ganin Yarinyar ba.”

 Yace

     “Mamie bazaki gane bane wallahi yarinyar was looking so innocent, Allah ina office sai tunanin abin nike, ni gabaki d’aya ya hanani sukuni, Mamie ya zanyi?

    Ya k’arashe maganar yana langwab’ar da kai, Uwa wani jinjiri.
“Hudu ka kwanatar da hankalinka, na fad’a maka ba wani abin tada hankali bane, watak’ila ma yarinyar ta yafe maka, shiya saka bata ce maka komai ba ta wuce abinta.”
By
(Mrs)

&

Sanam

[3/31, 5:39 PM] -Roshni: [3/26, 2:59 PM] ~Roshni~: [Sunday, March 26, 2017]
BAKIN GANGA
BY
MAMU

&

SANAM
                    <<<7>>>
***

     Haka Hudu ya wuni jiki a Mace, yana tunano ‘Yar Zamfarawa, duk motsin da yayi tana lik’e a ransa.

Wani irin Abu yake ji yana fiskarshi zuwa gareta, kamar wani magic, baya da kwanciyar hankali idan bai ganta ba, musamman wannan mafarkin da yayi da ita.
     Gashi Mamynshi ta kasa ta tsare, ta hana shi fita, a cewarta sai ya huta a weekend d’innan, ko b’angarensa hanashi fitowa tayi, komai na buk’ata aika masa ake yi.

    Hudu bai tab’a ganin Monday tayi masa nisan zuwa ba, irin wannan.

 Ya k’agara ya fita ofis yaje Gusau, ko mafarkinsa zai zama gaskiya.

“Haba Hudu ruwa kawai ka watsa mata fa, amma ka dame kanka, sai kace kad’eta kayi ta karye.”

Zuciyarshi tayi masa wannan tuni, amma shi kam ya kasa gane meke faruwa dashi.
*

      Misalin k’arfe 7:15am na safiyar Litinin (Monday), sai ga Hudu shar cikin shirinsa na fita ofis. Yayi b’angaren iyayensa ya gaidasu.
     Mamy sai mamaki takeyi, “sammakon meye haka na fita zuwa ofis hudu?”

Tayi mashi wannan tambayar tana ajiye carbin hannunta.

     “Wanda ke fita har after 9 yau shine before 8 ma zai fita.” yace mata “Wani aiki mai muhimmanci zaiyi a ofis yau.”
   Addu’ar kariya tayi masa, ya fice, ko break ya kasa tsayawa.

  

*

     Fitarshi daga Unguwarsu, hanyar barin gari ya d’auka, ko ofis baya jin zaya iya zuwa, sai yaje ya tabbatar da mafarkin da yayi.

     Tafiya kusan ta Sa’a d’aya (1hour) yayi, gaf da zai shiga Mafara sai ga kira daga ofis, cewar maza-maza yazo ana nemansa.

Ba yadda ya iya dole ya juya mota, ya dawo hanyar sokoto, yana ta tsaki, kwata-kwata an b’ata masa lissafi.
    Gudu yake ta shararawa, yazo sokoto yayi abinda zaiyi a ofis, ya juya Gusau.
*

 “Hamida! Hamida!! Hamida!!!”

Iman ce keta bud’ar bakin kiran Hamida, tazo tayi mata wankin kayan islamiyarta.

       Yarinyar tayi bala’in raina Hamida saboda irin cin mutuncin da taga mahaifiyarta nayi mata, bata la’akarin da fin shekarun da Hamida ta bata.
      Wanka Hamida takeyi, ai da sauri ta juye ruwan a jikinta, ta d’auro zani ta fito, tana karkarwar sanyi.

        “Lafiya kike k’wala min kira haka Imani?”

Cikin sanyin murya tayi mata wannan tambayar, tana tsane jikinta da k’aramin zane.

   Uniform d’inta ta watso mata a jiki, sai warin zufa (gumi) sukeyi, Hamida tayi saurin d’auke numfashinta.  Imani tace 

“Maza ki wanke min, idan sun bushe ki hura charcoal iron (dutsen garwashi) ki goge min, bana son kuma rashin hankali, don kika k’ona min kaya irin yadda kika yi kwanan baya zaki ga me zan maki a gidan nan.”
       Inna Larai dake cikin d’aki ta fito, tana tambayar lafiya Imani ke d’aga murya, itada waye?

     “Nida wannan jakar mana Inna, nayi mugun tsanarta.”

Wata dariya Inna ta kice da ita, “kiyi min maganinta kawai Imani, nima ba son bud’e ido nake na ganta ba, amma anyi kwantai sai lokacin sadaka ya sauka.”

   

  Tuni Hawaye sun fara yiwa Hamida ambaliya a fuska, har kirjinta take jin yana mata zafi, ta rasa me ta tsarewa wad’annan bayin Allah.

      Kwasar kayan tayi ta fara wankewa, tana tsartar da yawo, saboda Imani irin matan nan ne masu warin k’ashi.
*

Hudu kam gudun da yake shararawa na yayi sauri ya dawo sokoto har ya b’aci, ya take mota son ransa, kamar baya gudun faruwar wani Abu…..

[3/31, 5:39 PM] -Roshni: [3/31, 3:30 PM] -Roshni:
 BAKIN GANGA
By
Mamu

&

Sanam
                 <<<8>>>
***

      Gudu sosai Hudu yake shararawa, bai auni ba, sai jin yayi karo da wata mota mai zuwa .

Mai motar yayi over taking din wata mota, shi duk a tunaninsa Hudu ya ganshi, zai sauka a titi, ya bar masa wuri ya wuce, don har wuta ya matsa masa. 

Bai San Hudu hankalinsa yana sokoto ba, sai kaura da juna kawai suka ji sunyi.
      Dukansu Basu k’ara sanin inda Kansu yake ba, sai jama’a masu wucewa ne sukayi parking domin yin taimako, bayan motocinsu sun dame da juna.

     Da k’yar aka zaro kowannesu, sunyi jina-jina da jini, aka kwashesu aka k’arasu dasu sokoto, a asibitin U.D.U.T.H tare da taimakon ‘yan sanda na kusa.
*
     Accident & Emergency akayi dasu da gaggawa. Likitoci suka fara duba su.

Bayan awa biyu, likitoci suka gama duba su, kowannensu an  masa dressing duk inda suka ji ciwo, tare da allurori.
*
   Daga nan fa aka fara Neman ‘yan Uwansu, wancan d’ayan kam an samu ‘yan uwansa dake mafara, ta hanyar wayarsa dake jikinsa, sun kamo hanya suna ta kuka.
Matarsa Basira tana fad’in “Yanzun nan ya baro gida, har muna rikicin akan ba zanje bikin suna ba, na tsaya nayi masa tuwo kafin ya dawo, ni kuma na kafe sai naje ko bai barni fa.”

Ta fyace majina, tana kiran “Kar ka mutu Ashafa, na fasa zuwa bikin, kuma zanyi maka tuwon.”
      A hanyar zuwansu ne, sun kawo wurin da had’arin ya faru ne, suka ga yadda motocin suka yi, kai kace ba za’a samesu da rai ba.
Sosai suka k’ara rud’ewa, tare da b’arkewa da sabon kuka.

Basira sai fad’i take “Na zama Bazawara Ni Basira.”

Kakarsa ce ta kwab’e bakinta, tana ta sababi.
*   

    Hudu kam duka wayoyinsa rufe suke GAM da password, an rasa ya za’ayi a neme ‘yan uwansa, sai kashe wayoyin wata nurse take tana k’ara kunnawa, amma wayoyin sai nuna a saka password suke.

   

    Haka aka hak’ura har zuwa Yamma, babu abinyi, har hukumar asibitin tace za’a je a bada sanarwa, sai ga Mamy tayi kiransa, taji ko lafiya yake yau, ta jishi shiru.
    Da karkawa Nurse ta d’aga wayar, ganin sunan Mamy rubuce a screen din wayarsa d’aya.

   “Hello! Good Evening Ma’am.”

Nurse ta fad’a da sauri.

Tuni cikin Mamy ya kad’a, jin Mace ta d’auki wayar d’anta.

   “What is Happening to my Son pls? And Who are you?”

Mamy ta fad’a kamar ta fashe da kuka.”

         “Ma’am, Rush to the Hospital (U.D.U.T.H) now, your Son…..”

Ai Mamy bata Bari ta k’arasa bayanin ba, ta tsinke wayar, a guje ta dauko mayafi, ta fice a gidan ita da direba.

A hanya take kiran Daddy su had’e a asibitin.
     Tana shiga asibiti ta k’ara kiran wayar, Nurse d’in ce tayi mata kwatance har d’akin da yake, sai da ta iso k’ofar d’akin sannan ta katse kiran.
 Kuka sosai Mamy takeyi, ganin halin da hudu da yake ciki, ga drip an d’aura masa, ga bandage a hannu da k’afa.

Baccinsa yake yi bai san a ina yake ba.
A lokacin Daddy ya k’araso, Mamy ta fad’a jikinsa tana kuka, bata damu da jama’a dake wurin suna kallonsu ba, fad’i take “Pls ka gaya masa kada ya mutu ya barni. I can’t do with out Him.”

Har da had’awa da dukan kirjin Daddy.

    

Ganin jama’ar dake wurin hankalinsu ya dawo garesu, yasa Kunya ta rufe Daddy, ya jata zuwa cikin d’akin, yana lallashi.

Had’e da tambayarta “Ya abin ya faru?”

      Hawayenta ta goge, tace “Nima ban sani ba.”
Nurse din dake wurin ce tayi masu bayanin yadda abin ya faru, daga hanyar Mafara aka zo dasu, sunyi accident.

       Ido suka zaro, sanin su dai ba suyi da hudu ba, cewar zai je Gusau yau ba.

Ya saba duk zai je aikinsa na ofis, sai ya kirasu a waya sunyi masa Allah ya tsare hanya.
Ba abinda ya fad’owa Mamy a rai, sai yarinyar da hudu yake damuwa da ita kwanan nan, wacce ya watsawa ruwa.
     “‘Yar Zamfarawa”

Mamy ta furta a fili, ta juyu tana kallon Daddy sosai.

     “Aikam idan har zuwa wurinta ne Hudu ya had’u da wannan masifar, ba shakka Yarinyar ‘Yar Mayu ce, sai nasa an d’aureta daga ita har iyayenta.”

BAKIN GANGA 1&2

​[3/10, 1:41 PM] ~Mamu gal 💞: [Friday, March 10th, 2017]
BAKIN GANGA

By

Mamu
®NAGARTA WRITER’S ASSOCIATION.
***

                  ‹‹‹1›››
       Lemon kankana take kurb’awa a hankali, tana danna wayar dake hannunta. 

   Lokaci zuwa lokaci ta kan d’ora wayar a kunnenta na dama tana saukewa, guntun tsaki ta ja a karo ba adadi, saboda matsalar Network. 

     Banko k’ofar falonta akayi  daga k’ofar waje, da k’arfi.

Da sauri ta mayar da hankalinta zuwa wurin, domin ganin waye? 

    Mata biyu ne suka shigo cikin falon nata, a jikinsu  atamfa ce sanye garesu, zane iri d’aya, sai dai  kowa da kalar nashi. 

     K’ura masu ido tayi, tana jiran k’arin bayani, domin ta ji daga wacce duniya suke? 
    “Malama tun wuri ki fara had’a kayanki, domin ki bawa gidan wuri yasha iska, kafin mu k’araso ”
     D’aya daga cikin matan da suka shigo ta fad’a, tana yatsina, had’e da k’arewa falon kallo. 

    Doguwa ce, yar Siririya, ta rik’e k’ugu tana karkad’a jiki, kamar zata karye.  

   D’ayar kam, sai taunar chewing gum takeyi, tana k’as-k’as. Tare da toshe hanci da hannu d’aya, tana firfita da hannunta d’aya.

      Matar dake zaune a falonta, data dad’e da gane ko su waye. 

      Hakan yasa ta fara wayarta, taci sa’a wayar ya shiga yanzu.

Tayi kamar bata san akwai wata halitta a cikin falon nata ba.

       “Hajiya Nasara mun tashi lafiya?”

Ta fad’a, fuskarta cike da fara’a.

     Shiru tayi, tana sauraren ta cikin wayar, bayan sun gama gaisawa ne, suka fad’a maganar da zasu yi.

   Ta d’auki tsawon lokaci, tana wayar, jin sun samu irin kayan da suke so, kuma zasu samu riba sosai.

      ‘Yan matan kam iyanzu sun daskare a wurin, sai harara suke watsawa wacce suke tsaye a kanta.

   Ita kam tama manta da wasu wai a falon, tuni ta karkata hankalinta jin maganar Naira, sai lissafin kuddi suke yi.

     

    Bayan ta kammala wayar, ta shige kitchen d’inta, wurin d’ora girki, ta barsu nan a falo.

    Ganin da sukayi ta wulak’antasu, bata ko kallo gefensu ba, yasa suka hau borin kunya, suna cigaba da zage-zage har suka fice a cikin Falon, tare da banko k’ofa.
     Sosai take dauriya tun d’azo, jin ficewarsu ne yasa ta saki kuka mai cin rai, Wanda ana jinsa, za’a gane Wanda ke yinsa, damuwa tayi masa tarin yawa.
(Mrs)

[3/12, 2:38 PM] ~Mamu gal 💞: [3/12, 1:41 PM] ~Mamu gal 💞
BAKIN GANGA

By

Mamu
®N.W.A

              <<< 2>>>

***

     Zaune suke a kujera mai d’aukar mutum d’aya, suna farantawa juna rai, cike da soyayya mai tsayawa a rai.

     Sosai ta k’ura masa ido, wannan sajen na mijinta, ba k’aramin d’aukar mata da hankali yakeyi ba.

K’ura masa ido tayi k’irrrr, a k’alla na minti uku, ta shagala sosai da kallonsa, sai ji tayi yana hura mata iska a ido.
     Firgigit ta dawo hankalinta, fuskarta cike da murmushi, ta furta masa kalma mai tsada a birnin masoya.

“I love you.”

    Zama ya k’ara gyara mata a jikinsa, yace “I love you too.”

 Har yanzu murmushi ne kwance a fuskarta, ta k’ara furta masa “I love you more.” Tana lumshe ido.

    Zaro ido yayi kad’an, yace “No, I love more Sweet.”

 

     Jin tana k’ona hannunta ne da tukunyar da take girki, yasa tayi firgigit ta dawo daga duniyar tinanin da ta fad’a, na rayuwarsu ta baya da mijinta.
    Lokacin suna cikin gurzar amarcinsu, wannan Moment yak’i gogewa a brain d’inta.

    Kuka takeyi, tunawa a yau yadda mijin nata ya juya mata baya, yak’i d’aukar k’addarar da Ubangiji ya d’ora masu.
   Hmmmmmm! Lalle Ni Hamida na yarda da wannan Karin maganar na hausawa, cewa “NAMIJI BAKIN GANGA ne, a ko’ina ka buga zak’i zaka ji, idan kuwa ya juye maka, sai yafi d’an kunama zafi.”

   

   Murmushin takaici ta fitar, ta juye girkinta a cikin Warmers, ta shirya komai a inda ya dace.
  Ta b’ata lokaci sosai, wurin wankanta da shiryawa, ta dawo falo ta zauna, ta cigaba da kallonta, rik’e da carbi a hannunta tana ja.
 Bata fi minti sha biyar ba, taji dawowar mai gidanta.

A nitse ta tashi, tayi masa sannu da zuwa, ba yabo ba fallasa ya karb’a, ya shige ciki.

   Jiki a mace ta bisa har d’akinsa, wanka ta samu yanayi, sai ta fitar masa da kayan da zai saka, ta zauna zaman jiransa a bakin gado, tare da rafka tagumi.
    “Bana son wad’annan kayan, kinsan duk ba su nake ra’ayi ba.”

Hargowarsa ce ta dawo da ita daga duniyar tinani.

“Kayi hakuri, wanne zan Ciro maka?”

  Ta mik’e zuwa wurin drawer kayan sawarsa, tana tinanin, yaushe ne zata yiwa mijinta abinda zai faranta masa rai? 

      Da zafin nama ya tureta gefe, tare da nuna mata k’ofa.

“Fice min malama, ba abinda kika iya, baki San komai ba na farantawa miji, marar tarbiya kawai.”

     Da sauri ta juyo har tayi rabin fita d’akin, a gabansa ta tsaya.

“Yanzu nice marar tarbiya Hudu?”

Ta k’arashe maganar tana kuka, mai cin rai.

    “Lalle banyi mamakinka ba, saboda kai ne Wanda bai San k’addara ba, har kake neman kirana da wannan suna, any way, Nagode.”

    Da gudu ta fice a d’akin, ta fad’a nata d’akin, Wanda suke opposite da nashi, a yau tana dana sanin auren mutum mai Hali irin na mijinta, Wanda bai San kowacce k’addara ba, mai kyau ko akasin haka, da Allah yake d’orawa bayinsa ba, domin jarabawa.

***

ASALIN LABARI…..

(Mrs)

TABARYA MAI BAKI BIYU 111-115

​[1/24, 12:50 PM] Mamu: TAƁARYA MAI BAKI BIYU
©Mamu
®N.W.A
111-115
*
WASHE GARI

———————

Amarya da Ango na gani shar dasu, sai murmushin ƙauna suke dokawa juna.

    “Love da dadi.”

Cewar Adnan, yana ajiyewa amaryarsa break fast da ya haɗo masu.

   Bayan ya gama ciyar da amarsa taci ta ƙoshi, sannan shima yaci nasa, tana manne a gefensa.

    Maryam kanta a ƙasa tana wasa da ƴan yatsunta, kunya fal ta cikata.

   Motsi kaɗan tayi, sai ya tambaya, “Minene Amaryata?”

Kaɗa kanta kawai takeyi, alamar babu komai.
*

Yadda yaga safiya, haka yaga daren ranar, ko yaya ya kasa bacci, saboda azababen kishi.

  “Adnan am very sure next haduwarmu da kai, I will make your entire life so miserable, that’s my promise.”

 “That’s my promise.”

Abinda Ahmad ya kwana maimaitawa kenan, kamar sabon kamun hauka ya koma.

Sam baiyi tinanin yayi sallah ko addu’a akan Allah ya yaye masa halin da yake ciki.

   Ya tabbatar abinda yake yi dai ya saɓawa shari’ar musulunci.

Mutum da matarshi kace sai ka daukar masa action.
 KARFIN HALI BARAWO DA SALLAMA
*

Zaman hularsa yake gyarawa a gaban madubi, wacce ta shiga da kalar kayansa. Sanye yake da shadda kalar milk mai haske, yayi kyau sosai, Ango sak!

Maryam tana taimaka masa da fesa tirare.

   “Yanzu da gaske Moon baza tafi dani naga Ummata ba?”

Maryam ce tayi maganar, bayan ta ajiye tiraren hannunta akan madubi, da alamar shagwaɓa.

   “Yanzu Star ko nace zan tafi dake zaki bini, jiya-jiya fa kika baro gidan nan, yau kwananki daya jal a gidanki.”

   “Allah zanje Adnan.”

Idonta har sun fara cika da hawaye, ta kauce fuskarta gefe, tana kokarin ɓoyewa.

     Lallashi Adnan ya hau yi, bayan ya ɗauke hawayen dake zubo mata da yatsarshi ɗaya, sannan ya fice.

 Tare da abokansa zuwa wurin yiwa iyayen Maryam godiyar basu ƴa.

(Wannan al’adar sakkwatawa ne, musamman idan ango ya samu Amaryarsa cikakkiyar budurwa, shine ake zuwa yin godiya ga iyayenta, nuni da na sun bata tarbiya mai kyau.)
*

 Bayan ya fice ne, Maryam ta kwanta domin yin isasshen bacci, kafin ƴan ganin Amarya su fara zuwa.

    A can gida wurinsu Abba, sosai suka karɓi Adnan tare da abokansa cikin karamci, suna ta zuba godiya.

 Adnan kam kunya yake ji sosai, sai noƙe-noƙe yake yi, yana ɗago kansa suka haɗa ido da Abba, da sauri ya mayar da kansa ƙasa, yana murmushi.

    “Oh yanzu su Abba sun san abinda na yiwa ƴarsu.”

Adnan yayi wannan tinanin a ransa, yaji kamar yace kasa buɗe na shige cikinki.

   Bayan gaishe-gaishe, Abba ya jagorancesu har wurin iyaye mata, suka gaisa.

Nasiha sosai ake tayi masu, tare da masu fatan alkhairi, da zama lafiya.
*

Bayan wucewarsu Adnan ne, Umma ta tura wasu ƙannenta mata su biyu, Maman Junior da Maman Amatullah suje su dawo da Bahijja, tare da direban gidan.

 Dama sun gama yanke magana da Abba jiya da dare.

     Da sallama suka shiga gidan, amma ƙaƙarin aman Bahijja ya karɓa masu sallama.

Zagaye suke da ita, Baba, Inna da Mu’azzam, sai sannu suke zuba mata.

   Da saurinsu suka ƙarisa wurin, suna tambayar “waye ba lafiya?”
Ganin Bahijja suka yi yashe a ƙasa, rike da ciki tana juye-juyen azaba, amai ɗinma yaƙi fitowa, saboda ba komai a cikinta.

  Sannu suka hau zuba mata, suna jajen yaushe ciwon ya sameta.

Inna Luba ce ke masu bayanin, ta ɗan kwana biyu tana wannan amaye-amayen.

  “To taje asibiti kuwa?”

Uwar Amaa ta tambaya tana ɗagata daga ƙasa.

Baba Ummaru ya sunne kai ƙasa, yana waige-waige.

“Hajiya ba taje ba, bamu da…”

Inna Luba bata bari Baba Ummaru kwandala ya ƙarasa bayaninsa ba, tayi sauri ta katsesa.

  “Za’a je ko zuwa gobe ne hajiya.”

Zaro ido Maman junior tayi “gobe fa?”

“Haba dai, yarinya kamar zata amayu hanjinta kina maganar gobe.

kimtsata mu wuce asibiti, dama mun zo daukarta ne, ta koma gidan mijinta.”

     Baba Ummaru yana jin kalaman Uwar Amaah yaji kamar ya fara rawa, saboda dadi, ƴarsa zata koma gidan kuddi, ko ya samu yayi kuddi shima.

 Jiki na ɓari Inna ta kimtsa Bahijja, itama ta goga basilin a fuska da ƙafa, amma ba wanka, ta goga kwalli, suka fito waje.

    Sai ga Baba Ummaru da akwatin Bahijja yana kicaniyar sakawa a bayan mota, direbanne ya fito ya karɓa ya saka.

  Ɗaga masu hannu yake tayi, har suka gama shiga motar suka wuce.
*

Binciken farko da Likita yayi, ya nuna Bahijja tana da ciki, har na tsawon sati shidda.

Hohohoho! Ku zo kuga murna gun Bahijja da Inna, ko kunyarsu Uwar Amaah basu yi ba.

Magunguna aka bata, tare da gargadin ta riƙa cin abinci mai kyau mai gina jiki akai-akai.

Likitar taso ta tsayarsu asa mata drip ko Leda ɗaya ne, amma bau Bahijja taƙi zama, gidanta kawai take hangowa a yau.

Haka suka rankaya cike da albishir mai dadi.
*

“Umma me yasa kika ƙi gaya min wancan maras kunya yazo?”

Galala Umma ta saki baki tana kallon Ahmad.

“Mijin Yar uwarka kake zagi ba laifin tsaye bana kwance?’

Itama ta jefa masa tambaya.

  ” Yanzu saboda Allah Ahmad ba zaka yi murna ba, za’a mayar maka da matarka, sai wani bala’i kake tsirowa kanka, kula matar aure, yanzu kai idan akayi maka haka da taka matar zaka ji dadi ne?”

   Ƙasa Ahmad yayi da kansa kamar zai sa kuka, Uwa wani jinjiri, yayi lamo a gado idonsa a rufe.

   Jin an kwaɗa Uwar guɗa, yasa shi miƙewa zaune ba shiri, kallon Umma yayi “Ko Maryam ce aka dawo min da ita?”

Ya fada yana ƙoƙarin miƙewa tsaye.

  “Kaci gidanku Ahmad.”

Daƙuwa Umma tayi masa.

“Ungo kaji, a garin Arna muke ne?”

Wata guɗar aka kara saki, ana nufato gefen Ahmad, da sauri Umma ta fito, Ahmad na biye da ita a baya kamar jela.

Turus suka yi, ganin Inna Luba sai kar kace hanci take tana zuba guɗa.

   “Sannunku da zuwa.”

 Umma tayi karfin halin cewa, tana murmushi.

Amma a ranta tana tinanin me ya faru kuma?

  “Hajiya kiyi taki murna kema, duk mun zama kaka.”

Cewar Inna Luba, bayan ta tsaya da guɗar, sai washe baki take yi.

Kallon bangane ba Umma take mata, ganin haka yasa Maman junior tace “Bahijja ce da ciki.”

“Haba dan Allah?”

Umma ta tambaya tana ƙarewa Bahijja kallo, lallai kam ga alamu masu ciki nan ta gani da ita.

“Alhamdulillah.”

Umma ta hau maimaitawa, tana roƙon Allah ya raba lafiya.

Ko da ta juya wurin uban gayyar, babu shi, babu labarinshi.

  Da sauri tace “Mu shiga ciki mana, kar mu wahalar da Bahijja da tsayuwa.”

Zubewa sukayi a kujerun Falon, Bahijja kam har da kwanciya, sai wani langwaɓewa takeyi.

Bayan an gama gaisawa ne, umma ta miƙe tace “Bari na kawo mata wani abin taci, sai tasha Magani.”

Tana fita, suma su Maman junior suka bi bayanta.

  Daga ita sai Innarta aka bari a Falon, sai ƙarewa gidan kallo Inna keyi, tana jinjina kyaunsa.

   “Na roƙeki Bahijja da ki zauna gidan nan, ki tatso mana arzikinsu, kinga yanzu kema zaki haihu, muna da gado a gidan nan.”

Jin haka Bahijja ta ƙara washe baki, tace “Ki dai Inna sa ido kiyi kallo kawai, ai yanzu na ƙara yin kwas zamana a gida.”

Hararar wasa Inna ta hau yi mata, dai-dai nan wasu ƴan mata kawayen Maryam, suka dire masu kololin abinci da abin sha, suka fice.
*

Lashe fiye da rabin abincin suka yi tas! Saboda yunwar dake tare dasu.

Inna ta samu Leda ta juyewa Mu’azzam da aka baro gida tare da Baba.

“Toh Inna ki ɓoye ledar mana, kar su gani su mai damu acici.”

Cikin mayafinta ta ɓoye kuwa, suka yi sallama, dai-dai lokacin direba yayi sallama, ya kawo akwatin kayan Bahijja.

Karɓar akwatin Bahijja tayi, ta shige ɗakinta.

Bayan ta fito wanka, ta sha maganinta, ta karkaɗe gadonta ta ɗane.
   Inna ma tana yin sallama da Umma, ta fito, tare da alƙawarin dawowa a kaita gidan amarya Maryam.

direba aka saka ya mai data gida.
*

Daga shigar ƴan matan Amarya a gidan, suka hau shewa, samun Maryam da sukayi tana zuba bacci.

Dundu Auta ta ɗana mata a baya, a rikice ta tashi, tana kallonsu cike da harara.

“Lafiya zaku zo ku same mutum har gidan mijinsa kuyi masa rainin wayo.”

    Ta ƙarashe maganar tana miƙewa zaune.

Ihu haɗe da sowa ƴan matan suka ɗauka.

    “kaga matan Aure fa.”

Cewar ƴan matan.

“Ke me ya baki haka, kika rainamu daga shigowarki jiya.”

“Mai garinku ne ya bani da ƙaniya.”

Maryam ta shige toilet dinta, ta barsu da baki sake.

Jin zasu wuce, suna shirin fita ɗakin, suna tsine mata, tayi masu wulaƙanci wai, daga shigarta har ta nuna ta yafe.

  Ai da gudu ta fito, tana basu haƙuri.

    “Wasa fa nake maku chicks.”

Haka dai suka yi ta barkwancinsu, aka shiryawa Angwaye abinci mai daɗi.
*

BAYAN WATANNI BAKWAI

_____________________
Maryam ce zaune a falonta, ta gama shirya komai na gidanta, girki da sauransu.

   Adnan ya fito daga ɗakinsa yana shan ruwan gora, yana amsa waya.

A gefenta ya zauna har ya ƙarasa wayar, ya juyu da hankalinsa a wurinta.

    “Star wannan cikin fa ba ƙaramin kyau yayi maki ba, skin ɗinki sai glowing yake, gaki kin cika dam, kamar…..”

Sai yayi shiru yana dariya.

  Murguɗa masa baki ta hau yi na wasa, “Da ai ka ƙarasa, tunda kullum idan baka kirani ƴar lukuta ba, baka jin daɗi.”
 Haƙuri ya hau bayarwa.

Far tayi masa da sexy eyes ɗinta, alamar ta haƙura, amma kar a koma.

 “Ni dai muje ko so kake sai kowa ya gama zuwa dubiya mu bamu je ba.”

    Haka suka rankaya sai gidansu Maryam, wurin duba Bahijja da ciwon baya ya sata gaba, sai da sanda take iya miƙewa tsaye idan ta zauna.

    Bayan sun gama gaisawa da Umma, suka shiga part din Ahmad.

Zaune suka same Bahijja kuwa da ƴar sandarta a gefenta, Ahmad yana kujera daban yana kallo.

   Ahmad yana kulawa da Bahijja yanzu, saboda yadda yaga cikinsa na wahalar da ita.

   Bayan Maryam tayi sallama an bata izinin shiga ne suka gaisa, tayiwa Bahijja sannu, Ahmad kuma shima tayi masa jaje.

   Yana ganinta nutsuwarshi ta ƙwace masa, yadda ta cika dam, ga dan cikinta ya turo kadan.

Tana ta yi masa magana tare da Adnan take zai shigo ya gaishesu, bai ma San tana yi ba.

   Sai da Bahijja ta janyu hijabin da tayi sallah ɗazo, tace ya shigo ba komai.

Kan ya dawo hankalinsa, sai ganin Adnan yayi zaune a gabansa yana gaishesa.

Firgigit yayi ya dawo hankalinsa, ya amsa fuska a ɗaure.

(Shi fa ya tsane Adnan ɗin nan, yayi ta bincike a ofis ɗinsu, su yayi ya kamashi yana dulmiyar da gaskiya akan kuɗɗi, yadda wasu lauyoyi keyi, ya tona mai asiri, amma sai ya samu akasin haka, ya rasa ta ina zai rama abinda yayi masa.)

 Adnan ya yiwa Bahijja ya jiki ya fice.

Wani kallo da Maryam taga Ahmad na binta dashi yasa tayi saurin miƙewa, tayi masu sallama.

   “Honey Adnan akwai kirki.”

Bahijja ta faɗa tana cije baki, ita dai yayi mata komai tunda ya aure Maryam, ta yiwa mijinta nisa.

   “Tana nan yadda take a tsuke, ko irin dan cikar nan na Maryam ko masu ciki da keyi bata yi ba.”

A ransa ya faɗa, yaja tsaki a fili, ya bar mata Falon.
BAYAN SATI BIYU
Bahijja ta haifo ƴan tagwayenta mace da namiji, Mashaa Allah.

Ku zo kuga murna wurin Ahmad, wai yau shine ya zama Baba.

Wani irin son Bahijja yaji yana ratsa shi, kamar lokacin da sukayi haɗuwar farko, musamman da ya ganta tana shayar da babies dinsa.

Karɓarsu yayi, yayi ma kowanne huɗuba, namijin Muhammad, maccen Nana Khadija.

Ajiyesu yayi tare da addu’ar Allah ya raya mai ƴaƴansa, ya haɗe har matarsa ya rungumesu, yana furta mata  Kalmar “I love u.”
*

Ranar suna an sha bidiri, Inna luba da ƙyar aka hanata zuwa gidan Bahijja, wai ita sai tazo anyi komai gaban idonta.

Ga kajin da take ta hangowa za’a ci, sai da ta roƙi ƙanwarta ta ƙullo mata duk abinda aka ci a gidan sunan.
*

Maryam ma ta haifo nata Baby boy, aka raɗa masa sunan Abban su Ahmad da ya riƙeta da amana.

Ranar Adnan ma kamar ya kyautar da kansa yake ji, saboda tsabar murna.

KARSHE.
NOTE

———————

 Zuwa ga makaranta wannan littafi, ina Neman afuwarku a jinkiren da kuka ta samu na wannan buk, ina Neman afuwa.
JAN HANKALI
Wannan labari “True life story” ne, sai dai ƴan ƙare-ƙare da aka samu.

Ha’inci baya da dadi ko kadan, wacce abin ya faru da ita, har takardar saki ta samu ga mijinta, saboda tayi masa cin amana da “PUSH UP”.

 Abinda yake faruwa yanzu kenan, mafi yawan mazan yanzu jikinmu da muke bayyana masu shi yake Jan ra’ayinsu garemu.

Amma da mun rufawa kanmu asiri, jikinmu a rufe, duk abinda mijinki ya gani dashi zaiyi amfani, amma kinzo kin nuna masa abubuwa, yazo yaga basu bane, me kike nufin zai faru???
Kuskuren da nayi a wannan buk ina rokon Allah ya yafe min.

Mu’assalam.

TAB’ARYA MAI BAKI BIYU 106-110

​[1/13, 11:24 AM] Mamu:
TAƁARYA MAI BAKI BIYU
©Mamu
®N.W.A
106-110
*******

       Mafi yawa daga cikin mutanen dake wurin ɗaurin auren, Hankalinsu ya tashi da jin furucin Abba.

     “Ahmad ya mutu.”

Da sauri Abba ya juya ya koma ciki, hankalinsa a tashe.

Mutanen da ke wurin, suka rufawa Abba baya.

    Masu zuba sauri nayi, haka ma masu gudu duk suna yi, da ƙyar suka gansu ɗakin. Ɗauko Ahmad akayi kamar Baby, aka ɗora a mota, sai asibiti.

    A hanya Abba ya samu ya kira Umma, domin gaya mata abinda ake ciki.

Faɗi yake “Hajiya Ahmad lokaci yayi, ya haɗiye zuciya ya mutu.”

      “Innalillahi wa’ina illahi raji’un.”

Abinda Umma ta san ta iya faɗa kenan, ta zube a kujera, tana rusar kuka.

    Kafin kace kwabo! Gidan biki ya juye ya zama gidan koke-koke.

Babu ɓata lokaci su Umma suka bi bayan su Abba a asibiti.
*

 U.D.U.T.H
Da gudu Nurses suke tura Ahmad saman gadon majinyata, aka shige dashi emergency, tare da rufe ƙofa.

    Abba kamar ya saka kuka, A cikin ransa yana tausayin ɗansa, kuma ya san duk halin da Ahmad ya shiga, shi ya jefa kansa, tun farko sai da aka haɗasu da yarinyar nan, ya tozartata, ya kawo zaɓinsa, yanzu don ta kwaɓe masa yake son yayi ruining life na Maryam.

    “Dole ma ya ɗauki kaddara, domin yin hakan, shine cikar imanin kowanne Bawa.”

Abba ya faɗi haka a hankali, yana zama saman kujerar ƙarfen dake ƙofar emergency.

     Dai-dai nan su Umma suka iso, tana share hawaye, ana riƙe da ita.

   “Alhaji ina gawarsa?”

Umma ta tambaya, idanuwanta na ƙara cika da wasu hawaye.

   Cikin mutanen da suka taimakawa Abba ya kawo Ahmad asibiti, wani ya bata amsa “In shaa Allah bai mutu ba Hajiya, suma ne yayi, zai farfado.”

Wani sanyi suka ji da bayanin wannan mutumin.

    Bude ƙofar da akayi ta ɗakin da Ahmad yake ciki, yasa kowannensu ya tinkare wurin likitan, ana tambayarsa ya ake ciki?

    “Likita ya mutu ko?”

Tambayar da Abba ya watsawa likita kenan. gabansa yana faɗuwa, yana jiran muguwar amsa.

    “Kai ne ubansa?”

Likitan ya tambaya, yana gyaran zaman farar rigarsa irinta likitoci.

“Eh nine likita, ga kuma Uwarsa anan.”

Ya nuna masa Ummah.

     “To Ku biyoni a ofis ɗina.”

*
 “Wato yaronku ya samu big shock ne, Allah ya tsare, domin irin hakanne ake rasa mutum baki ɗaya.”

    Kallon juna Umma da Abba sukayi a tare.

“Yanzu dai mun dai-daita komai, yana bacci, kowanne lokaci zai iya farkawa.”

   Cewar likita yana cigaba da rubuce-rubuce a takardun marasa lafiya.

  “Amma shawarar da zan baku, kuyi ƙoƙari ko bashi abinda yake so.”

   Godiya su Abba suka yiwa likita, jiki a mace suka fito, zuwa ɗakin da aka kwantar da Ahmad.

Bacci yakeyi, ganin hakan Abba ya bar Umma a wajensa, shi kuma zai koma gida ya sallame jama’a.

     Da Abba zai dawo ne yazo da Amarya, ba yadda baiyi ba ta zauna ta ƙi, dole yazo da ita.

    Ko da suka ƙarasu, sun samu Adnan Ango da family and friends ɗinshi, suma sun zo dubiya.

 Ango sai watsawa amaryarsa kallon ƙauna yake, itama dai sai murmushi takeyi ƙasa-ƙasa.

Da Yamma aka bawa Ahmad sallama.
*

8:00pm motocin ɗaukar Amarya suka zo, Amarya tasha kuka kamar me, amma haka sai da aka rabata da Ummarta da gidansu, zuwa wani sabon wuri a gareta.

  Bayan an wuce da Amarya ne, Umma ta shiga ta Ƙara duba Ahmad, kwance ta samesa yana ƙaƙarin amai, ba mai taimako.

    “Ina Bahijja Ahmad?”

Umma ta tambaya cikin mamaki, ita dai ko a asibiti bata ga Bahijja ba, kai ko a shagalin biki babu ita.

   “Umma bata nan, tafi sati….”

Bai ƙarasa maganar ba, sai amai, ya harar da duk maganin da yasha.

    Umma ta gyara mai jiki da wurin, tana mamakin yaushe Ahmad zai samu kwanciyar hankali a gidansa?

     “Gobe za’a je a dawo maka da matarka.”

Kamar a sama yaji maganar Umma, sai dai ba yadda ya iya, dole yayi shiru.

       “Umma ina Maryam?”

Ahmad yayi wannan tambayar bayan ya ɗan jingina da pillow yana mayar da numfashi na aman da yayi.

      “Amarya kam yanzu tana gidan Angonta Ahmad.”

Umma ta cigaba da yi masa nasiha na ya cire matar wani a ransa.

   Shiru Ahmad yayi kamar mai bacci, har Umma ta ɗauka ko ya samu bacci ne, ta tofeshi da addu’a tare da rufesa da bargo, ta fice.

    Ahmad kam tinanin yake idan ya haɗo da Adnan next me zai masa ya huce????

TABARYA MAI BAKI BIYU 95-105

​[10/24, 2:29 PM] Mamu.: [10/24, 2016   11:39 AM] Mamu.: TAƁARYA MAI BAKI BIYU
©Mamu
® N.W.A
          96-100
*****

GAISUWA a gareki (Sophie durling) kin fi kowa son littafi nan.
*****
    “Hello My Star……”

Kalmar da Adnan keta maimaitawa amma yaji shiru, hakan yasa ya tsinke wayar, yace ko matsalar network ne, kara kira yayi back, amma yaji wayar a rufe.

    Dan tsaki yaja, yace matsalar nan ta network tana damun al’umma, ina tsakar waya da masoyiya ta, ya ɓata min show, juyawa yayi ya koma cikin kotu, bakin aikinsa.

      Dama anje break ne ya samu chance na waya da Maryam.

Shigewa yayi ciki, yana gyara zaman hularshi da rigarshi, na lawya.
*

       “Don Allah meye haka Ya Ahmad?”

Maryam ta tambaya, fuskarta na nuna alamar rashin tsoro tattare da ita, amma fa zuciyarta sai bugawa yake yi da ƙarfi.

        Wani murmushi Ahmad ya fitar mai sauti kaɗan, ya ajiye wayar kan madubi, ya juyu yana kallonta.

      “Idan kinga mun fita ɗakin nan, to an shafa fatihar ɗauren aurenmu.”

     A kiɗime Maryam tace ” kai da waye?”

Sai da Ahmad ya gyara kwanciyarshi saman gado, sannan yace mata “Ni dake mana.”

   Zumbur ta miƙe daga kan kujerar da take, ta zube a kasa, tana kuka tana roƙonsa, kar yayi mata haka, kada ya rabata da masoyinta.

     Ta yaya za’a ce ya rufesu cikin ɗaki daga shi sai ita, yace ba zai buɗesu ba, sai an ɗaura masu aure?

       Juya mata baya Ahmad yayi, ita kuwa duk inda ya juya sai binsa take yi tana roƙo, amma Ahmad yayi mata kamar kurma.

      Can dabara ta fado mata, da gudu tayi wurin ƙofar ɗakin tana bugu, ko Allah zai sa wani yaji, azo a buɗesu.

      Cikin zafin nama Ahmad ya mike daga kan gadon, yayi wurinta, fisgarta yayi daga bakin ƙofar, ya jefata kan gado, yana huci.

      Kuka sosai Maryam takeyi yanzu, tsoronta bata San abinda Ahmad zai aikata mata ba, jikinta ko’ina sai rawa yake yi.

     Gyara tsayuwarshi yayi a kanta, yana ƙare mata kallo, doguwa riga ce a jikinta, Bata fitar da surarta ba, sai dai babu ɗankwali a kanta, gashinta yasha retouching sai kyalli yakeyi, sai yanzu Ahmad ya lura ashe tana da gashi mai tsayi kaɗan.
       Cikin karfin Hali ta buɗe baki ta fara magana

“Ya Ahmad idan kan cutar dani wallahi Allah ba zai ƙyaleka ba, saboda me zaka hanani auren Wanda nake so? Kai ba ka aure wadda kake so ba?”
      “Enough.”

Ya Daka mata tsawa.

“Ina son Maryam yanzu, itama dole sai na aureta, kin gane ko, ko tana sona ko bata sona, dole na aure ta.”

      Tinani Maryam ta fara yi, anya Ahmad bai fara kurbe-kurben zamani ba, da zuke-zuke.

    Idonta a waje take ƙare masa kallo, lallai taga changes a jikinsa, yayi duhu kuma ya rame.

     Addu’o’in tsari ta fara jerowa cikin zuciyarta, tana Neman Allah ya kawo mata mafita.
       K’arar murda ƙofar da suka ji ne, kowannensu yasa hankalinsa ya koma a ƙofar.

    “Lafiya? Me ya samu ƙofar nan, ban jima da  barin ɗakin nan ba, yanzu kuma na dawo na tarar dashi a kulle.”

Cewar UMMA mamaki shinfide a fuskarta, ita dai tasan a buɗe tabar ƙofar,amma yanzu har da key.

             “Waye a ciki?”

Umma ta tambaya.

     Maryam tana jin muryar Umma ta tsala uban ihu

 “UMMA ki bude nice Maryam da Ya…..”

Kan ta ƙarasa Ahmad ya hau gadon ya toshe mata baki.

     Ƙwanƙwasa ƙofar Umma ta hau yi kamar zata karyata, tana kiran sunan Maryam.

   Jin haka duk sauran mutanen da basu watse ba, suka fito domin jin ba’asi.

    “Lafiya Aisha kike dukan ƙofar ɗakinki haka, ƙin buɗewa yayi ne ko me?”

Cewar Abba yana ƙarasowa wurin.

    “Ina fa lafiya Alhaji, Maryam ce a ciki da wani ya rufe ta, ɗazo tayi magana, amma yanzu naji shiru.”

     Kan taƙarasa Abba ma ya hau dukan ƙofar, yana kiran sunan Maryam, hankalinsu idan yayi dubu ya tashi.

     Wata murmushi Ahmad ya saki, yace “Dama haka nake so.”

 Yana gama faɗar haka ya saki bakin Maryam, ya taka har zuwa bakin kofar ɗakin ya tsaya.

    Ɗaga murya yayi sama, yadda za’a ji shi sosai yace, “Abba!

Umma!

 idan kuna so na buɓe ƙofar nan, to yanzu Ku kira mutane a shafa fatihar aurenmu nida Maryam, idan ba haka ba, sai dai mu tabbata a ɗakin nan, amma ba inda zamu fito.”

    Salati mutanen wuren suka ɗauka, jin muryar Ahmad.

Ashe dama shine ya rufe Maryam cikin ɗaki?

   Yanzu kam suna jin muryar kukan Maryam, kuka takeyi sosai mai cin rai.

    Abba yace “Yanzu Ahmad rashin hankalinka har ya kaika da yin wannan iskancin, to yau kuwa zamu gamo da kai, dani kake zancen.”

Abba yana gama magana ya juya yayi ɗakinsa.

    Gyara zama Ahmad yayi bakin ƙofar, yana jiran amincewarsu.

     Umma kam kuka take yi, tana faɗin, a taimaka a fito mata da yarta, kar Ahmad yayi mata illah.

   Wata yayar Umma ta matso kusa da ƙofar.

” Ahmad kana jina, ka bude kofar nan, mu zauna muyi wannan maganar cikin fahimta, zan tsaya maka kai da fata.”
    “No!”

Ahmad ya faɗa da ƙarfi har yana mikewa a tsaye.

“Ba fa zan buɗe ƙofar nan ba, sai an ɗaura mana aure nida Maryam.”

   Ba irin dadin bakin da basu yiwa Ahmad ba, iyayen da ƴan matan, amma yayi kunnen uwar shegu dasu.

       Da gudu Maryam ta tashi ta shige toilet dake cikin ɗakin, ta murza key.

Ta shammaci Ahmad kam, don ko da yazo kamo ta, yayi latti.

Ƙwafa yayi, yace “ai dai muna ɗaki ɗaya, ba inda zaki fita yarinya, sai kin zama mallakina.”

   

     Da sauri Abba ya dawo, ko da yazo wasu har sun gaji da tsayuwa sun zauna a wurin, UMMA ce kawai a tsaye da sauran mutane kaɗan, suna ta mamakin wannan al’amari.

        Jayewa sukayi, suka bawa Abba wuri, spare key dinda ya ɗauko yasa, yana murzawa.

Ƙarar da Ahmad yaji ana buɗe k’ofa yasa shi sauren kai idonsa a kofar, ko da ya karaso har Abba ya bude kofar, yana turawa sai ga Ahmad tsaye tsuru-tsuru.

     Mari mai kyau Abba ya wanka masa.

“Mu sa’annin wasanka ne Ahmad?

Abba ya tambaya da ƙaraji.

    Dai-dai nan duk su umma suka shigo dakin, wasu suka tsaya shiga tsakanin Abba da Ahmad dake ta shan maruka, wasu kam sukayi wurin Neman Maryam, cikin masu Neman Maryam Umma ce a gaba.

      

     ” ina ka kai min yarinya?”

“Me kayi mata Ahmad”

Umma ke tambayarsa hankali a tashe.

Bayan sun duba, ba Maryam a ɗakin.

     Da gudu Maryam ta fito daga toilet, tayi wurin Umma tana ta kuka, ta ƙamƙameta.

      Gaba daya zagaye Maryam sukayi suna duba lafiyarta, har Abba ya baro wurin Ahmad, yazo dubata.

“Ba abinda yayi maki Maryam?”

   Gyada kai tayi alamar “Eh.”

Juyuwar sa zasu yi, ba Ahmad a ɗakin.

Da sauri duk suka fito waje, har falo ba Ahmad.

    Nan suka zube ana mamakin wannan Abu da Ahmad yayi.

    Abba kam ƙin zama yayi, yace sai yabi Ahmad har part ɗinsa, yaci masa mutunci.

     Wata ƙanwar Abba tace “wai ni yaushe Ahmad ya dawo yana son Maryam, ina cewa da ƙinta yayi?”

     Cikin fada Abba yace “Rashin ta ido irin ta yaran yanzu ne.”

   Nan aka gaya masu ga abinda ke faruwa, majority ɗinsu duk basa bayan Ahmad, duk sun goyi bayan a nuna mai kuskurensa da yayi tun FARKO.

       Umma ita dai tana rungume da ƴarta har yanzu, sai a nan take tambayarta ya haka ta faru?

Maryam tana share ƙwalla da bayan hannunta, tayi masu bayanin yadda abin ya faru.

     Abba ya ƙara zabura, da ƙyar aka kwantar dashi, cewa ya kyale Ahmad, ai zai fito ne ya gamu dasu.
*

Tana tsaka da loda kuddinta cikin jakarta ta hannu, saboda yau ta samu Chance, Ahmad ya ɗaga daga ɗakin, don haka zata ɗiba da dan yawa, yadda zasu yi mata kwana biyu.

     Ta cika Jakarta Dam! Zata rufe drawer kenan, Ahmad ya fado dakin…                                      Kallon-kallon suka tsaya yiwa juna, Bahijja gata tsoro-tsoro gaban drawer, ga kuddi cike da jaka ba tayi zipping ba.
     “SATA.”

“Ahmad ya fada da ƙarfi.”

    Jikin Bahijja ba inda baya rawa, ta durkushe a wurin, ta fara kuka, don tasan yau kam ta gama yawo.

    “Don Allah kayi haƙuri.”

Shi kawai ta iya furtawa, sai matsar ƙwallar da take yi.

      Kafin ta kara wani tinani, sai ga Ahmad a gabanta, yana wani irin huci, tana kallon fuskarsa ta kara shan jinin jikinta.

    Mari ya kwada mata, sai da taga stars suna yawo a sararin samaniya.

Duk haushin da Ahmad ya kwaso sai da ya saukewa Bahijja shi a jiki.

     “Baƙar mata, nikam tunda na hadu dake duk komai nawa ya lalace, na rasa wacce nake muradi saboda kin yaudareni, kinyi min acuci, yanzu kuma sata kike min, kafin kizo ki fara kisa, saboda mugun son kuddinki.”

    Ahmad yana huci, muryarsa ko fita ba tayi sosai, sabada bala’i, baƙin ciki goma da ashirin, sun haɗe masa.
    “Wallahi sai na aure Maryam, ba zata aure Adnan ba.”
Abinda Ahmad ke faɗa kenan, yana rinbiɗar Bahijja.

   Tuni Bahijja ta gigice, ga baƙin ciki rashin kuddinta, ga wata magana da taji Ahmad na fada, kenan ya dawo son Maryam.

         “TIƘISA.”

Sai Bahijja taji tafi jin ciwon kalaman akan dukan.

      Kamar kayan wanki haka Ahmad ya jata ya fito da ita har get, ya jefa mata hijabi, daga ita sai kayan jikinta take, yace tayi gidansu a koya mata tarbiya.

Kuka takeyi kamar me, ta samu Napep da ƙyar, saboda yanayin unguwar.

Duk Wanda ya wuce ta a hanya sai ya dauka iyayenta ne suka mutu, yadda take gurza irin wannan kukan.

      A ƙofar gidansu ta sauka, tace mai Napep ya jirata, ta karɓo mai kuddinsa, don bata da ko ficika.

Tana kuka ta shiga gidan, Inna luba dake wanki tsakar gida ta tare ta.

      “Lafiya kike wannan kukan Bahijja.”

Bata samu cewa komai ba, sai gunjin kukanta da ta ƙara.

    Dai-dai nan Baba Ummaru ya fito daga banɗaki, daga gani wanka yayu, na shirin fita kasuwa.

     Da sauri ya ajiye bokiti da container na sabulu, ya ƙaraso wurinsu.

Jikinsa har rawa yakeyi ya fara tambayarta

    “Ahmad din assiden (Accident) yayi ya mutu ko rauni yaji?”

Gabanshi na tsananin faɗuwa yayi wannan tambayar, baya fatan tambayarsa ta zama gaskiya, saboda har yanzu bai samu abinda yake tsammani ba, daga surikan nashi, ba labarin arzki, komai shiru.

     Muryarta ya tsinkayo tana cewa “ai gwanda ya mutu da wannan bala’i, ko ba komai nasan zanyi masa takaba na yagi rabona.”

      Ido waje Inna luba tace “karki cemin sakinki yayi.”

Hannu ta ɗora a kai ta kurma ihun, “mun shiga uku mun lalace malam.”

Ta ƙarasa tana kallonsa, wanka ya fito yanzu, amma sai da zufa ta fara fito masa.

 

      Cikin kuka Bahijja tace “cewa yayi nazo gida a koya min tarbiya wai.”

    Baba Ummaru sai gashi a kasa yana shan ruwan wankin Inna data zubar.

“Alhamdulillah tunda bai ce yayi saki ba.”

    Inna luba tace “wai me ya kawo haka?”

Bahijja bata tsaya komai ba tace “Bakar shawararki Inna ta ɓata komai…..”

Kan ta ƙarasa inna ta toshe mata baki

      “muje ɗaki.”

Inna ta faɗa tare da fisgar Bahijja suka shige ɗaki.

Baba Ummaru yabi bayansu har yana rafka tuntube, domin yaji wacce shawara ce Inna luba ta bawa Bahijja, har zata kashe mata aure.
      Ɗan Napep yaji shiru, oda yake matsawa ko ta ina, hakan yasa Bahijja ta tuna dashi.

Kallon Inna tayi, “aika masa Dari biyu.”

Da Sauri Baba Ummaru ya juya zuwa waje.

Bayan ya sallame mai Napep ya dawo cikin gida, maganganun da yaji su Bahijja nayi yasa shi tsayuwa a wurin……
(Mrs)

[11/5, 5:32 PM] Mamu.: [11/5, 5:11 PM] Mamu.: [11/3, 6:13 PM] Mamu.: [11/3, 4:49 PM] Mamu.: TAƁARYA MAI BAKI BIYU
© Maryam Alƙali (Mamu)
® N.W.A
101-105
****

“Inna kuɗɗinsa fa ya kama ni ina ɗauka, shawarar dai da kika bani….”

      Bahijja bata ƙarasa maganarta ba, taji tafin hannun Baba yana sallalami.

      “Yanzu dama sata kike masa?”

Baba Umaru ya faɗa fuskarshi cike da mamaki. 

Gyaɗa kai ya cigaba dayi, daga bisani ya fisgo Bahijja, ya murɗe mata kunne ɗaya.

    “ƙaryarki tasha ƙarya, ki hanani yin arziki, ashe wannan dalili ne ya hana yaron ko alkhairi baya mana, ashe baƙin hali kika je masa dashi.”

    Da sauri Inna luba ta shiga tsakaninsu, tana janye hannunsa daga kunnen Bahijja, wadda kamar ta saki fitsari take ji, saboda zafin da kunnenta yakeyi.

       Haki sosai Baba yakeyi, yana masifa yana kumfar baki, wai shi an hanasa yin arziki. Da ƙyar ya sakar ma Bahijja kunne.

    “Wai dan Allah malam wake bawa wani arziki idan ba Allah?

Tambayar da Inna tayi masa kenan.

      Cikinta yayu kamar zai cinyeta ɗanya, yace duk abinda Bahijja tayi, to training ɗinta ne ai.

    Inna Luba tuni ta shige gashi, jin asirinta yana neman buɗewa, ga wani kallo da Bahijja ke watso mata, wanda da hankalin Baba Umaru a kwance yake da ya gane dawan garin.

     Ranar dai haka Baba Umaru ya bar gidan yana ta ɗan neman zage-zage.

Bayan fitarshi ne, suka fara ƙulla shawarar meye abin yi.

    Dogon nazarin da Inna Luba tayi, ta samu masu mafita.

Mafitar ɗaya ce, za’a yiwa Ahmad kiranye, dole zai zo da ƙafarsa yana neman gafararta.

 

*

 “ƙarbi ki shanye yanzu ki bani kofi nayi gaba.”

Cewar Umma, tana miƙawa Maryam wani ɗan madaidaicin ƙofi, cike da tsumin ɓaure da kaninfari, yasha mazarkwaila sai ƙamshi yakeyi, ga sanyi.

    Kamar Maryam tayi kuka, haka ta karɓi kofin ta fara sha.

Umma na tsaye a kanta, sai da ta shanye tas ta miƙawa mata kofi, sannan Umma ta juya ta fice daga ɗakin.

    Murmushi Maryam tayi, da ta tuna Adnan ɗinta ake yiwa wannan gyaran, kuma tsimin fa daɗinshi take ji ma a baki, amma kullum idan Umma ta bata sai tayi gulma.

     Gidansu ya fara cika da ƴan uwa na nesa, na kusa ma wasu sun fara hallara.

Sai shirye-shirye akeyi, bikin saura sati ɗaya.

     Gefen Ahmad kam yaga dai ba makawa rasa Maryam zaiyi, wannan dalilin yasa zazzafan zazzaɓi ya rufeshi, amma a gidan ba wanda ya sani, saboda duk sun zama Busy, gashi Bahijja bata nan.

    Shi kaɗai yake rayuwarshi, ciwo yana damunshi, ba magani ba abinci, duk yayi zuru-zuru.

Sai yunwa tayi kamar zata kashe shi, zai je kitchen da ƙyar ya haɗa ruwan Tea yasha.
 *

BAYAN KWANA UKU.
Zaune suke kowaccensu ta rafka uban tagumi.

 Tun wayewar safiyar yau, har kawo yanzu ƙarfe Hudu saura, ko kwarar hatsi bai ga cikinsu ba, sai ruwa suke kwarawa hanjinsu, duk cike ya ƙulle.

    Shararaf-shararaf ya shigo gidan, misalin shidda na yamma, ko salama bai samu yi ba, ya zube jagwab a tabarmar dake shimfiɗe a tsakar gidan, yana ƙare masu kallo.

    Suma dai kallon suka bishi dashi, ganin ya shigo Empty hand, ba komai wanda ya riƙo.
Mu’azzam ne yace “Baba naje na ɗauko kaya a waje?

Yunwa tun ɗazo muke ji, kaga Anti Bahijja sai Aman ruwa takeyi, saboda su kaɗai ke garemu a gidan nan.”

     Inna Luba kam ba bakin magana, jikinta sai rawa yakeyi, Ulcer ɗinta ya tashi.

Da ƙyar ta yunƙora ta tashi ta zauna.

      “Malam bamu taɓa irin wannan ƙuncin ba, me yake faruwa ne haka?”

    Bahijja ya nuna mata, “Wannan Almurar ce, gayyar tsiya.”

Tuni ya fara haki, saboda shima ba komai a cikinsa, wani maƙocinsa ne a kasuwa ya siya shinkafar Hamsin, yaci ya rage masa, cokali hudu ya samu ya kora da ruwan bota.

  “Wannan rashin kuddin da ake ciki, mutane na neman na abinci, wa zai kula da wani siyan magani.”

Ido Inna Luba ta ƙwalalo, tare da faɗin “Mun shiga uku.”

     Yunƙurin aman Bahijja ya juyu dasu, suka riƙeta, sai ƙaƙari takeyi komai yaƙi fita.

Kuka sosai Mu’azzam yasa yana birgima a ƙasa, shi abinci.

      Sallama yaro yayi ya shigo gidan, ɗari biyu ce a hannunsa, ya miƙawa Inna luba.

Ƙarɓa tayi tana jiran bayani, a ranta kam murna fal.

   “Na zakka ne, na gidan Alhaji Mai Mota, ya rabawa ƴan unguwa, zakka ya fitar.”

Da gudu yaron ya juya ya fita.

    Da sauri Baba Umaru ya fisge kuddin, ya zira silifas ɗinshi ya fice a gidan.

Garin kwaki ya auno masu ya dawo, ya koma massalaci don sallatar magrib.

      Ko sallah su Inna basu tsaya yi ba, suka hau sarrafa kwakinsu, bayan sun kammala su hau kansa, ba sauƙi.

    Bahijja tana ci tana kuka, tana tuna irin abincin gidanta, da acan take me zai hana ta girka kalar abincin da take so ta ci.

    Inna tana jin sheshsheƙar kukanta, ta hau lallashinta, cewar komai ya kusa zuwa ƙarshe.

Baba kam yana shigowa ya hau ta da faɗa, jin abinda yake faruwa, inda yake shiga ba nan yake fita ba. Abincin ma kasa cinyewa tayi, ji tayi zuciyarta na tashi.

Baba Ummaru da Mu’azzam suka ƙarasa cinyewa.
 *

Taro yayi taro, wurin cike yake da jama’a maƙil, kusan yawan jama’ar mutanen wurin sunyi ado cikin manyan kaya irin na al’adarmu na Hausa/Fulani.

       Abba ma ya ƙure adaka cikin wata dakakkiyar shadda fara, sai ƙyalli takeyi.

Ya fito a Uban Amarya tsaf.

 Ɗaurin Auren Maryam kenan da Adnan.

      Bayan an kammala ɗaurin aure akan sadaki dubu Hamsin.

Mutane suka fara taya Ango Adnan murna da uban Amarya, sai da Abba ya natsa ya duba iya hangensa, amma bai hango Ahmad ba.

     Wannan dalilin yasa shi zage jiki yayi hanyar gefen Ahmad, domin yaji meye hujjarshi na ƙin zuwa ɗaurin aure.

 Kwance ya sameshi kamar matacce, Abba ya ɗauka bacci yakeyi.

    Saboda yayi sallama har ya gaji ya ji shiru, wannan dalilin yasa shi kutsa kai a cikin ɗakin Ahmad.

        Da isarshi wurinshi ya daka masa tsawa, amma yaga Ahmad da ƙyar ya buɗe idanuwanshi, wadanda ke nuna jin jikin da yakeyi.

     “Abba ka taimakeni ka aura min Maryam kar na mutu, wallahi sonta yana wahalar dani.”

Da ƙyar Ahmad ya furta waɗannan kalamai, yana cije baki, ya yunƙura zai tashi zaune, amma ya kasa.

      “Kayi istigfari Ahmad, mun riga mun shaida Maryam ta zama matar Adnan, yanzu nan.”

Abba ya faɗa yana jin tausayin yaronshi, ganin halin da yake ciki.

     Numfashinsa suka dinga kokawa, daga jin kalaman Abba.

Sai ga idanuwansa sun ƙafe, Abba na ganin haka, ya ruɗe.

     Jijjigashi yakeyi yana kiran sunanshi, amma Ahmad ina! Ko gezau.

Da gudu Abba ya bar ɗakin, Babbar rigarshi har tana cika da iska, ya dawo wurin jama’ar ɗaurin aure.

Faɗi yake “Jama’a ku taimaka min ɗana Ahmad ya mutu a ɗaki.”

TABARYA MAI BAKI BIYU 91-95

​[10/17, 9:36 PM] Mamu.: TAB’ARYA MAI BAKI BIYU..
©Mamu
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
91-95
***

ASSALAMU ALAIKUM
DAGA FARKO, ZAN FARA BAWA MASU KARANTA WANNAN LITTAFI HAK’URI, SABODA RASHIN SAMUNSA DA KUKA YI, AK’ALLA NAFI WATA BANYI TYPING BA, HAKAN YA FARU NE SABODA RASHIN JIN DADIN JIKINA DA BANA YI.

AMMA YANZU ALHAMDULILLAH.
*

“Haba UMMA, Don Allah ku tausayawa yaronku, Wanda shikenan Allah ya mallaka maku a gidan nan, na duniya.”

Ahmad ya fad’a yana zubar da hawaye sosai, yana kallon Ummarsa, haƙiƙa yasan akwai tausayi mai yawa tsakanin D’A da MAHAIFIYA.

     Zuciyar UMMA kuwa tayi rauni, har taji kamar ta zubar da hawaye, saboda tausayin Ahmad, Abba ne yayi mata wani kallo mai cike da alamomi iri-iri.

     “Ahmad maza-maza tashi kabar falon nan, kuma kar k’ara tada mana wata maganar aurenka da Maryam.”

     Cikin tsawa Abba yake maganar, har da mik’ewa tsaye, yana nunawa Ahmad k’ofa.

    Umma kam kauda fuskarta tayi gefe, tana share hawaye a b’oye.

    Kuka yake yi kamar ƙaramin yaro, ya miƙe, yana jan k’afa, kamar Wanda k’wai ya fashewa a ciki, yana tafiya yana waiwayo iyayensa.

   Ganin haka yasa Abba ya taso k’eyarsa har waje, sannan ya koma cikin falon ya rufe k’ofa, har da saka key.
*

  “Hajiya mai kike yi haka?”

Ko kuma nace me hakan ke nufi?

Kina so ki nuna min kinfi son Ahmad akan Maryam?

Kin manta wulaƙancin da yaron nan yayi tayi mata, yarinyar nan ƴar albarka duk ta shanye, ta nuna komai ba komai bane, tayi haƙuri ta rungume kaddara, sai yanzu ta samu mai sonta, zatayi aurenta ta huta, shikenan yanzu daga ganin ɗanki ya dawo zaiyi son kai, sai ki biye masa.”

     Kamu hannunta yayi yana murzawa a hankali, yana ƙare mata kallo, ganin yadda hawaye ke shirin zubo mata, amma tana ƙoƙarin mai dasu.

     “Haba Aisha, ki tuna yarinyar nan marainiya ce, kuma amana ce a hannunmu, amanar da zamuyi bayaninta a gaban ALLAH, idan muka bi son ranmu haƙiƙa zamuyi nadama.

    Kuma ya zama dole mu nunawa Ahmad kuskurenshi da yayi tun farko, yadda gaba zai kula.”

       Sosai Umma ta ɓarke da kuka yanzu, tana bawa Abba haƙuri, lalle taso tayi kuskure, ta inda soyayyar uwa ta rufe mata ido, amma komai yazo da sauƙi, tunda Allah ya haɗata da adalin miji, mai riƙon amana da hangen nesa.

     Abba yaji dadin yadda Umma ta dawo hanya, nan da nan suka cigaba da hirar yadda bikin zai tafi, basa son ma a ɗauki dogon lokaci wurin saka rana, indai ƴan gidan angon sun shirya.

A cewarsu gwanda ayi bikin kowa ya huta.
*

Ahmad dake zaune jikin ƙofa, bayan Abba ya rufe, ya samu wuri bakin kofar ya zauna, duk yana jin maganarsu, nan take yaji duk tsanar kanshi ta rufesa, yayi ta dana sanin me yasa yaƙi Maryam tun farko? 

   Amsa ya baiwa kansa da kansa, saboda ya tsaya yin zaɓen mai shape, at d end aka cuce sa.

    Cizon ɗan yatsa yake tayi, har ya koma part ɗinsa, ji yake kamar yasa caja ko dorina yayi ta dukan kansa, ko ya rage jin wani haushi, amma ba hali.

    Kwantawa yayi saman gadonsa yana juyi, ya rufe kansa da bargo, mafita yake nema, amma ya rasa ta ina zai ɓullowa al’amarin.
*

BAYAN SATI ƊAƳA.
An kawo sadakin Maryam dubu Hamsin, haɗe da sweet da goro, har an saka date na biki, nan da wata biyu.

Haka ma za’a kawo kayan akwati (Lehe) nan da 2 weeks.

    Murna wurin Adnan kamar me, gani yake kamar mafarki yakeyi zai farka, rawar jiki kowa Maryam tana Shanta, komai tace ayi, “Done.” yake cewa.

     A gefen Maryam itama sai shirye-shirye takeyi, itada ƙawayenta, su shiga nan su fita can.

    Umma ta mayar da hankali itama, sai gyaran ƴarta take yi, dama sakkwatawa ba dai gyara ba, indai za’a yiwa ƴaransu aure, tun da sauran lokaci ake fara tsumasu, irin abubuwan da ba zasu yiwa yaransu illah ba.
*

Bahijja duniya ta juya mata, ga ƙoshi ga kwanan yunw.

 Ta samu da ƙyar suka samu maganin da zasu riƙa facaka da kuddi, sun Shiga sun fita.

Amma Sam! Ahmad yanzu ko kallonta ba yayi, kullum yana ɗakinsa kwance, yana aikin tinani.

   Iyakarta dashi ta ƙare abinci ta kai masa ɗaki, wani zubin yaci, wani zubin akasin haka.

    Ko taje ɗaƙinsa kwana korar kare yake mata, tayi kuka har ta gode Allah.

    Tayi masa tambayar meke damunshi a duniyar nan, yayi mata banza, kunnen uwar shegu.

Gashi suna son kuddi ita da Inna, wayar safe daban ta rana daban, ta rasa ya zatayi da ranta, ita tama kasa gane me Inna zatayi da kuddi.

   Ahmad ɗin ma yaƙi ɗagawa daga ɗakin nasa, ballantana ta samu tayi ɗan hali.

 Ko ofis ya daina fita, ita ko ciwo yakeyi oho?

       Haka dai ta ɗaure ta shirya tana jin haushinsa, ta shiga cikin gida, yau ne kawo lehen Maryam.

    Ita fa, tayi bala’in tsanar Maryam, saboda Ahmad ya gaya mata, ita akaso ya aura yaƙi, ya auro ta.

   Shiyasa ko da ta shigo gidan ba ruwanta da sabgarsu, saboda tasan basa sonta.

 Har murna takeyi, da Umma ta gaya mata kwanan nan za’ayi auren Maryam. 
*

Mashaa Allah!!!

 An kawo kaya, sunyi kyau sosai, kowa sai yabawa yakeyi.

Bayan ƴan gidansu Adnan sun wuce da sha tara ta arziki, da aka shirya masu.        

      Su Umma sun shiga ciki tare da ƙannenta da yayyenta, suna ƙara shawarar biki.

    Falon ya rage Sai ƴan ƴara matasa haka.

  Bahijja yar mulki, tana hakimce a kujera, komai taƙi ɗagawa cikin kayan, sai kallo kayan takeyi a wulakance.

    Wannan dalilin ne yasa, wasu daga cikin danginsu, waɗanda basa iya gani su ƙyale, suka riƙa mata habaici.

“Wai ɗan talaka bai iya shiga arziki ba, sai yaga yafi kowa.”

     Bahijja ta shiga maida masu martani.

“Meye amfanin kuddin da ba’a ci, ai gwanda talaucin.”

Cewar Bahijja tana wani irin huci.

Dariya kusan rabin falon aka kwashe da ita.

   “Mu dai idan baki ci kuddinmu ba, to ke kika zo da mugun halinki, wanda yasa aka hana maki.”

Faɗin wata ƴar budurwa tana zazzagar jiki.

    Ai kuwa Bahijja ta rufe ido,  tana sauke masu haushin ɗan uwansu.

Suna maida mata martani.

    Jin hayaniya yasa Umma fitowa, da wasu sauran manyan anties, ana neman ba’asi.

   Bakin Bahijja yafi na kowa tashi, al’amarin da ya ƙara bawa mutanen falon mamaki, kamar ba gidan surakanta ba.

   Da ƙyar aka kashe wutar rigimar dai, Umma tace Bahijja ta koma gidanta, bayan ta bawa ƴan matan rashin gaskiya.

     Bahijja ta shure takalminta ta wuce, tana huci, baƙin ciki kamar ta juya ta cije bayanta.
*

Misalin 5:00pm na ranar,  Ahmad yayi ƙarfin halin shiga cikin gidansu, ba kowa a falo, hakan yasa yayi hanyar dakin Umma.

     Ɗakin Umma ya shige, yaci karo da Maryam tana zaune tana waya da Adnan,  saboda ɗakinta cike yake da ƴan mata, sai tsokanata sukeyi, sunki bari ma taji abinda Adnan yake fada, shiyasa ta gudu dakin Umma, tana wayarta hankali kwance,sai narke murya takeyi.

    Ganin mutum kawai tayi akanta yana huci, kamar mayunwancin zaki.

    Kwace wayar yayi, ya koma ya rufe kofar dakin, tuni jikin Maryam ya hau ɓari, hakuri ta shiga bashi, akan kar yayi mata wani abu…..
(Mrs)

TABARYA MAI BAKI BIYU 91-95

​[10/17, 9:36 PM] Mamu.: TAB’ARYA MAI BAKI BIYU..
©Mamu
®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
91-95
***

ASSALAMU ALAIKUM
DAGA FARKO, ZAN FARA BAWA MASU KARANTA WANNAN LITTAFI HAK’URI, SABODA RASHIN SAMUNSA DA KUKA YI, AK’ALLA NAFI WATA BANYI TYPING BA, HAKAN YA FARU NE SABODA RASHIN JIN DADIN JIKINA DA BANA YI.

AMMA YANZU ALHAMDULILLAH.
*

“Haba UMMA, Don Allah ku tausayawa yaronku, Wanda shikenan Allah ya mallaka maku a gidan nan, na duniya.”

Ahmad ya fad’a yana zubar da hawaye sosai, yana kallon Ummarsa, haƙiƙa yasan akwai tausayi mai yawa tsakanin D’A da MAHAIFIYA.

     Zuciyar UMMA kuwa tayi rauni, har taji kamar ta zubar da hawaye, saboda tausayin Ahmad, Abba ne yayi mata wani kallo mai cike da alamomi iri-iri.

     “Ahmad maza-maza tashi kabar falon nan, kuma kar k’ara tada mana wata maganar aurenka da Maryam.”

     Cikin tsawa Abba yake maganar, har da mik’ewa tsaye, yana nunawa Ahmad k’ofa.

    Umma kam kauda fuskarta tayi gefe, tana share hawaye a b’oye.

    Kuka yake yi kamar ƙaramin yaro, ya miƙe, yana jan k’afa, kamar Wanda k’wai ya fashewa a ciki, yana tafiya yana waiwayo iyayensa.

   Ganin haka yasa Abba ya taso k’eyarsa har waje, sannan ya koma cikin falon ya rufe k’ofa, har da saka key.
*

  “Hajiya mai kike yi haka?”

Ko kuma nace me hakan ke nufi?

Kina so ki nuna min kinfi son Ahmad akan Maryam?

Kin manta wulaƙancin da yaron nan yayi tayi mata, yarinyar nan ƴar albarka duk ta shanye, ta nuna komai ba komai bane, tayi haƙuri ta rungume kaddara, sai yanzu ta samu mai sonta, zatayi aurenta ta huta, shikenan yanzu daga ganin ɗanki ya dawo zaiyi son kai, sai ki biye masa.”

     Kamu hannunta yayi yana murzawa a hankali, yana ƙare mata kallo, ganin yadda hawaye ke shirin zubo mata, amma tana ƙoƙarin mai dasu.

     “Haba Aisha, ki tuna yarinyar nan marainiya ce, kuma amana ce a hannunmu, amanar da zamuyi bayaninta a gaban ALLAH, idan muka bi son ranmu haƙiƙa zamuyi nadama.

    Kuma ya zama dole mu nunawa Ahmad kuskurenshi da yayi tun farko, yadda gaba zai kula.”

       Sosai Umma ta ɓarke da kuka yanzu, tana bawa Abba haƙuri, lalle taso tayi kuskure, ta inda soyayyar uwa ta rufe mata ido, amma komai yazo da sauƙi, tunda Allah ya haɗata da adalin miji, mai riƙon amana da hangen nesa.

     Abba yaji dadin yadda Umma ta dawo hanya, nan da nan suka cigaba da hirar yadda bikin zai tafi, basa son ma a ɗauki dogon lokaci wurin saka rana, indai ƴan gidan angon sun shirya.

A cewarsu gwanda ayi bikin kowa ya huta.
*

Ahmad dake zaune jikin ƙofa, bayan Abba ya rufe, ya samu wuri bakin kofar ya zauna, duk yana jin maganarsu, nan take yaji duk tsanar kanshi ta rufesa, yayi ta dana sanin me yasa yaƙi Maryam tun farko? 

   Amsa ya baiwa kansa da kansa, saboda ya tsaya yin zaɓen mai shape, at d end aka cuce sa.

    Cizon ɗan yatsa yake tayi, har ya koma part ɗinsa, ji yake kamar yasa caja ko dorina yayi ta dukan kansa, ko ya rage jin wani haushi, amma ba hali.

    Kwantawa yayi saman gadonsa yana juyi, ya rufe kansa da bargo, mafita yake nema, amma ya rasa ta ina zai ɓullowa al’amarin.
*

BAYAN SATI ƊAƳA.
An kawo sadakin Maryam dubu Hamsin, haɗe da sweet da goro, har an saka date na biki, nan da wata biyu.

Haka ma za’a kawo kayan akwati (Lehe) nan da 2 weeks.

    Murna wurin Adnan kamar me, gani yake kamar mafarki yakeyi zai farka, rawar jiki kowa Maryam tana Shanta, komai tace ayi, “Done.” yake cewa.

     A gefen Maryam itama sai shirye-shirye takeyi, itada ƙawayenta, su shiga nan su fita can.

    Umma ta mayar da hankali itama, sai gyaran ƴarta take yi, dama sakkwatawa ba dai gyara ba, indai za’a yiwa ƴaransu aure, tun da sauran lokaci ake fara tsumasu, irin abubuwan da ba zasu yiwa yaransu illah ba.
*

Bahijja duniya ta juya mata, ga ƙoshi ga kwanan yunw.

 Ta samu da ƙyar suka samu maganin da zasu riƙa facaka da kuddi, sun Shiga sun fita.

Amma Sam! Ahmad yanzu ko kallonta ba yayi, kullum yana ɗakinsa kwance, yana aikin tinani.

   Iyakarta dashi ta ƙare abinci ta kai masa ɗaki, wani zubin yaci, wani zubin akasin haka.

    Ko taje ɗaƙinsa kwana korar kare yake mata, tayi kuka har ta gode Allah.

    Tayi masa tambayar meke damunshi a duniyar nan, yayi mata banza, kunnen uwar shegu.

Gashi suna son kuddi ita da Inna, wayar safe daban ta rana daban, ta rasa ya zatayi da ranta, ita tama kasa gane me Inna zatayi da kuddi.

   Ahmad ɗin ma yaƙi ɗagawa daga ɗakin nasa, ballantana ta samu tayi ɗan hali.

 Ko ofis ya daina fita, ita ko ciwo yakeyi oho?

       Haka dai ta ɗaure ta shirya tana jin haushinsa, ta shiga cikin gida, yau ne kawo lehen Maryam.

    Ita fa, tayi bala’in tsanar Maryam, saboda Ahmad ya gaya mata, ita akaso ya aura yaƙi, ya auro ta.

   Shiyasa ko da ta shigo gidan ba ruwanta da sabgarsu, saboda tasan basa sonta.

 Har murna takeyi, da Umma ta gaya mata kwanan nan za’ayi auren Maryam. 
*

Mashaa Allah!!!

 An kawo kaya, sunyi kyau sosai, kowa sai yabawa yakeyi.

Bayan ƴan gidansu Adnan sun wuce da sha tara ta arziki, da aka shirya masu.        

      Su Umma sun shiga ciki tare da ƙannenta da yayyenta, suna ƙara shawarar biki.

    Falon ya rage Sai ƴan ƴara matasa haka.

  Bahijja yar mulki, tana hakimce a kujera, komai taƙi ɗagawa cikin kayan, sai kallo kayan takeyi a wulakance.

    Wannan dalilin ne yasa, wasu daga cikin danginsu, waɗanda basa iya gani su ƙyale, suka riƙa mata habaici.

“Wai ɗan talaka bai iya shiga arziki ba, sai yaga yafi kowa.”

     Bahijja ta shiga maida masu martani.

“Meye amfanin kuddin da ba’a ci, ai gwanda talaucin.”

Cewar Bahijja tana wani irin huci.

Dariya kusan rabin falon aka kwashe da ita.

   “Mu dai idan baki ci kuddinmu ba, to ke kika zo da mugun halinki, wanda yasa aka hana maki.”

Faɗin wata ƴar budurwa tana zazzagar jiki.

    Ai kuwa Bahijja ta rufe ido,  tana sauke masu haushin ɗan uwansu.

Suna maida mata martani.

    Jin hayaniya yasa Umma fitowa, da wasu sauran manyan anties, ana neman ba’asi.

   Bakin Bahijja yafi na kowa tashi, al’amarin da ya ƙara bawa mutanen falon mamaki, kamar ba gidan surakanta ba.

   Da ƙyar aka kashe wutar rigimar dai, Umma tace Bahijja ta koma gidanta, bayan ta bawa ƴan matan rashin gaskiya.

     Bahijja ta shure takalminta ta wuce, tana huci, baƙin ciki kamar ta juya ta cije bayanta.
*

Misalin 5:00pm na ranar,  Ahmad yayi ƙarfin halin shiga cikin gidansu, ba kowa a falo, hakan yasa yayi hanyar dakin Umma.

     Ɗakin Umma ya shige, yaci karo da Maryam tana zaune tana waya da Adnan,  saboda ɗakinta cike yake da ƴan mata, sai tsokanata sukeyi, sunki bari ma taji abinda Adnan yake fada, shiyasa ta gudu dakin Umma, tana wayarta hankali kwance,sai narke murya takeyi.

    Ganin mutum kawai tayi akanta yana huci, kamar mayunwancin zaki.

    Kwace wayar yayi, ya koma ya rufe kofar dakin, tuni jikin Maryam ya hau ɓari, hakuri ta shiga bashi, akan kar yayi mata wani abu…..
(Mrs)

TAB’ARYA MAI BAKI BIYU 86-90

​[9/7, 4:05 PM] Mamu 🤓:
 TAƁARYA MAI BAKI BIYU
© Maryam Alƙali (Mamu)
® N.W.A
86-90

****

Ƙarfe biyar da rabi na yamma, Maryam ce zaune a falo tare da Ummah, suna kallo.

Bayan ta dawo daga makaranta, ta watsa ruwa taci abinci.

Zaune take kan kujera mai cin mutum ɗaya, yayin da Umma ke kan mai cin mutum biyu.

  Tana so ta faɗawa Umma wata magana, amma sai nauyi take ji.

Bakinta sai motsi yakeyi, amma ta kasa furta kalma ɗaya.

    Ganin haka yasa Umma ta fahimce bakin ƴarta da magana, yasa ta maida nutsuwarta a gareta.

    “Maryam ya naga kamar da abinda kike so ki faɗa, amma kuma kinyi shiru?”

A sokwane Maryam ta ƙara duƙar da kanta ƙasa, tana Murmushin kunya.

“Dama-Dama…..”

      Umma ta katseta tana murmushi itama, “Haba ƴata! Yau kuma Ni ake kunya kuma, feel free ki gaya min abinda ke damunki mana.”

Umma ta ƙarashe maganar tana dafa cinyar Maryam, haɗe da riƙe hannunta na dama, tana mata Murmushi mai gamsarwa.

    “Ammmmm Ummah dama Adnan ne yace, yana so ku bashi dama zai turo magabatansa.”

     Tana kaiwa nan, tayi ƙasa da kanta, cike da kunyar abinda zata aikata masu.

Na bijirewa auren ɗansu.

     “Kai Mashaa Allahu, nayi murna sosai ƴar autana zata yi aure, Allah ya sanya alkhairi, idan Abbanku ya shigo anjima zan sanar mashi.”

Sosai Umma ta nuna Murnarta a fili, wanda hakan ya bawa Maryam kunya, da gudu ta shige ɗakinta, tana sauke numfashin murna.

    Bayan shigar Maryam ɗaki, Umma sosai tayi mamakin wannan lamari, to ya haka? Yaushe Maryam ta daina son Ahmad har take iƙirarin auren Adnan? 

   Tasan waye Adnan, tuntuni yake bibiyar Maryam, amma ganin hankalinta baya kansa, shiyasa basuyi mata dole ba, a lokacin da Ahmad ya ƙi ta.
*

   “Guess What Moon ?”

A gefe ɗaya cikin wayar, yace  ” Na baki gari star.”

    Dariya ta saki mai sauti, ta cigaba da ja masa rai, inda daga ƙarshe ta zayyane masa komai.

     “Abba ya amince daka turo magabatanka, a gidansu Maryam Anas Yaro Sifawa.”

Wani tsalle Adnan ya daka, yana cikin chamber, koda suke waya da Maryam,  hakan ne yaja hankalin yan uwansa lauyoyi dake cikin chamber ɗin, ganin haka yasa Adnan ya fito a 360 ya kawo cikin motarsa, ya buɗe ya shiga.

    “Are u serious Star?”

Ya tambaya yana mayarda numfashi, a gefe ɗaya kuma, yana ganin kamar mafarki yakeyi, wai yau Maryam ce da kanta, take gaya masa zata auresa.

      “Surprise.”

Ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya.

     A gefe ɗaya shima Adnan yana tayata, lallai yau akwai kwanan farin ciki a garesu.
*

Misalin ƙarfe 8:30 na dare, Kwanon sha da murfinsa ne riƙe a hannunta, an rubuceshi ciki da bai, fal da rubutun wasu ayoyin Al-ƙur’ani da tawadda.

Wanke rubutun tayi tas! Ta kwankwade, tana sha tana kiran sunan Ahmad, tana lissafo buƙatarta garesa.

      Bayan ta adana kwanon, tayi shigewa toilet, ta tsalo wanka.

Kwalliya tayi cikin fitinannun kayan bacci, sai ƙamshin Humrarta na haɗi take zubawa, bayan ta gama kimtsawa, ta fice zuwa ɗakin mai gidanta, wanda wannan shine karonfa na farko, data kai kanta ɗakin miji.

     Sosai ɗakin yayi mata kyau, yadda ta gyareshi ɗazo, bin lafiyar gado tayi, bayan ta kunna tv dake cikin ɗakin.

Tana kallon tashar MBC bollywood, har bacci ya fara fizgarta.
*

   Ƙarar buɗe ƙofa da taji, ya farkar da ita.

Daga banɗaki ya fito, jikinsa duk lemar ruwa ne, da hannu ɗaya yana tsane kansa da ƙaramin towel.

    Wani irin shauƙin sonsa taji yana malalar mata, yana bin jini da tsokarta.

Sai wani lumshe ido takeyi, tana binsa da kallo.

     Bata ma san shigowarsa gidan ba, gashi kuwa da alamu ya daɗe da shigowa a gidan.

    Sarai ya ganta, amma shi kam yanzu ba ita bace a gabansa, (Maryamu ta jatau kyawu ya hana taɓawa) itace muradinsa.

So kawai yake ya gama shirinsa, yajewa mahaifansa da maganarta, shi fa ko bata sonsa sai anyi aurensu.

    Jinta kawai yayi, tana shafa masa lotion a jiki, cikin wani irin salo na ɗaukar hankali.

Ga wani ƙamshi nata mai jan ra’ayi.

Gashi sai wani jujjuya jiki takeyi, haɗe da lum-lumshe idanuwanta kamar mai jin bacci.

“Lallai fa yau sai ta gwada maganin nan, taga ko zasu dace.”

Hakan ta ayyana a zuciyarta.

     Babu shiri babu tsammani, sai ga lamari ya juye zuwa inda ba’a zata ba.
*

   Ƙarfe 5:30 na asuba, suka farka, a tare suka tashi, bayan sunyi sallah, sai fa sannan Ahmad ya tuna da abinda ya wakana.

    Sosai yaji haushin kansa da bai je wurin Abba ba, a daren jiya, anyi wacce za’ayi.

   A ɓangaren Bahijja kam, buƙata ta biya, don Ahmad yayi mata alƙawalin abinda take so.

    Zumbur! Ya miƙe, da shirinsa na zuwa wurin mahaifansa.

Gabansa Bahijja tasha, ganin zai fice, ta tuna masa da alƙawarinta.

 Baya so ta ɓata masa lokaci, shi yasa kawai  ya ɗauko kuddi ya miƙa mata, domin dama yasan abinda take buƙata kenan.

 Yasa kai ya fice, zuwa sashen iyayensa, babu ɓata lokaci.
*

   “Abba dama magana nake so nayi daku.”

Cewar Ahmad yana sosa ƙeya, bayan ya gama gaishe da mahaifansa, tare da tabbatar da sun tashi lafiya.

     Sun kuwa tattaro duka hankalinsu suka bashi, suna saurarensa.

  “Dama maganar Maryam ce, ina so Abba ku aura min ita, kuma ina roƙonku don Allah kada ku duba laifina na baya, ai duk ɗaya muke nida Maryam.”

  Cike da mamaki, Umma ta kallo Abba, shima ita yake kallo.

“Wacce Maryam kake nufi Ahmad.”

Cewar Abba yana mamaki.

“Abba Maryam ƴarku ta nan gidan, wadda kuka so aura min a baya naƙi, yanzu na dawo hanya, ina sonta Abba.”

     “Ahmad Anya kai ne kuwa???”

Umma itama ta faɗa tana zaro idanuwa a waje.

   “Wallahi Allah nine Umma ɗanki. Na tuba, nabi Allah na biku a yanzu, don Allah ku aura min Maryam, a yanzu ina matuƙar ƙaunarta.”

   “Anya kana d isasshiyar kunya Ahmad??”

Umma ta ƙara tambayarsa, ranta yana tafarfasa, saboda tasan duk abinda ya faru laifin Ahmad ne.

  “Wai Ahmad kasan Maryam ɗinda kake magana a yanzu, wani take so, har ta gabatar dashi a garemu, har fa an saka date na Engagement a jiya.”

 A firgice Ahmad ya ɗago, ya zubawa iyayensa idanuwansa da suka kaɗa sukayi jajir, da ƙyar ya buɗe baki ya fara magana…..
Blog: mrsjabo.wordpress.com

TAB’ARYA MAI BAKI BIYU 81-85

​[8/28, 5:48 PM] Mamu 🤓
 TAƁARYA MAI BAKI BIYU…
©Maryam Alƙali (Mamu)
®N.W.A
81-85
*****

Babu abinda bakin Ahmad ke fitarwa sa Murmushin Alƙhairi, ganin Maryam zaune front seat nasa.

Macen da ya tsana a baya, yau gashi ya waye gari, yana muradinta a gefensa, a matsayin matarsa ta sunnah.
Ya juyo ta gefenta yafi a ƙirga, ganin bata da niyyar daina latsar wayarta, yasa shi gyaran Murya, haɗe da kiran sunanta cikin wata soft voice.

“Maryam.”

Bata daina abinda takeyi ba, ta karɓa masa.

“Na’am ya Ahmad.”

Maida hankalinsa yayi ga tuƙensa.
Yayi ta maza ya ɗaure, yace “shin ko kinsan na kamu da sonki a halin yanzu.”
Ajiye wayarta tayi, saman kafafunta, ta saka Hannu ta zaro kunnenta waje, ƙila kaurin pashmina ɗinta ne yasa taji kamar Ahmad yace yana sonta.

Dai-dai nan Ahmad ya juyu yana kallonta.

“U heard whats am saying, so pls stop pretending kamar baki ji ba.”

Ya furta, yana wani malalacin murmushi, mai haɗe da dana sani.
Kallo sosai Maryam ke binsa dashi, irin kallon nan na ka kamu da taɓin hankali, daga bisani ta gyara zama.

Tana wani irin murmushi, ta juyu tana kallonsa da kyau.
Ganin haka Ahmad yasa shi fara Hamdala a zuciyarsa, yana da confidence still she’s loving and waiting for him, ol dis while.
“Ya Ahmad na maka murna, da wannan abu daka tsince zuciyarka a ciki, amma tabbas Maryam tayi maka nisa yanzu, Maryam’s Heart is belong to some one now, not u.”
Wani wawan burki Ahmad ya taka a tsakiyar titi, jin maganganu Maryam, kamar saukar aradu a ka.

Allah yasa ba mota a kusa  da shi.

Juyuwa yayi yana kallonta, alamu ya nuna ya manta a ina yake.

Ita kam Murmushi take tayi, fararen haƙoranta sai sheƙe sukeyi.
Ruwan Horn da aka riƙa watsawa Ahmad ta ko’ina, ba shiri ya sashi gangarawa gefen hanya, yayi parking.

Mutanen dake bayansa suka soma wucewa, suna ta zaginsa, zai kawo masu hatsari.
Idanunsa ya fara murzawa, wai ko mafarki yake yi, ya farka, amma ina!

Ga Maryam nan zaune a gabansa, ta kafesa da sexy eyes nata, still kuma sai Murmushi take masa.
He’s spechless, wai yau Maryam dai daya raina a baya, yau itace take murɗa masa kambonta son ranta.

Jin ana taba ƙofa yasa ya kai idanuwansa ga wajen, saman hannun Maryam ya sauke idanuwansa da sukayi jazir, ran maza ya ɓaci, tana ƙoƙarin buɗe ƙofar, ga alamu fita take ƙoƙarin yi.
Tana kallon agogon wayanta, tana ƙoƙarin buɗe ƙofa, tace masa “Yaya, i have to go, zanyi late.”

Bai ce mata komai ba, ya yiwa motar key, hakan yasa ta gyara zamanta, ta cigaba da latsar wayarta.
A zuciyarta tace, HaƘuri mai daɗi kenan.

A baya nayi kukan zuci dana fili, yanzu kuma is ur turn Ya Ahmad.

Wannan tinani da tayi yasa ta saki Murmushi mai sauti.

“Wa kike wa dariya a nan?”

Ahmad ya tambaya cike da ɓacin rai.”
Kallonsa tayi, jin tsawar daya daka mata, ta haɗiye dariyarta, tunawa da itace fa ƙwailar da yake ƙi a baya, yanzu kuma saboda tace tana son wani, shine har da kishinta.

“Allah baka haƙuri, nida friends ɗina ne.”

Shiru yayi mata, ya ƙara speed, kamar zai tashi dasu sama, ko zasu bar garin.
Minti biyar, sai gasu a ƙofar makarantarsu, bayan ya shiga cikin school, yayi Parking, tana jiran ya cire lock ta fita, kamar a sama taji yace mata

“Shi wanda kike so yanzu, a anan makarantar yake?”
Sai da ta sakar mai murmushi mai kyau, ta kaɗa idonta, suka ƙara lumshewa, sanna ta bashi amsa

“Barrister ne mai zaman kansa, he’s name Adnan.”
Wani tari yazowa Ahmad, yi yake ba ƙaƙƙautawa, ya rasa na miye??

A wannan hali Maryam ta bude ƙofa, ta fito daga cikin motar.

Ɗan ranƙwafuwa tayi, dai-dai gilashin motar, tace masa “Thanƙs.”

Tana ɗan ɗaga masa fingers nata, cike da yanga.
Sauke ajiyar zuciya Ahmad yayi, yana mai ƙissimawa ransa, dole Maryam ta auresa, ko tana so, ko bata so.

Ya fige motarsa da gudun bala’i, ya bar makarantar,

Inda kowa ke kauce masa, kar yaji mai ciwo.
 *

Extra key ɗinta ta ɗauka, don rana irinta yau kawai, tayi hanyar ɗakinsa.

Zatonta yazo dai-dai, ɗakin a rufe yake gam!

Ta ciro key ɗinta ta buɗe, dube-dube take tayi a ɗakin, ta rasa da ina zata farawa, ga jikinta sai ɓari yake yi, ita kam tunda Allah ya halicceta bata taɓa ɗaukar abun wani ba, sai yau zata fara, shiyasa jikinta ko’ina sai gumi yake fitarwa.
Haka tayi ƙarfin hali, ta fara bincike bedside drawers amma bata ga komai ba.

Taje wurin ƙofa ta leƙa ba ƙowa, ta dawo taci gaba da duba sif, kayan Ahmad ne jere sun sha guga, buɗe wancan rufe wannan, haka ta dinga yi har ta cire rai da ganin kuddi, sai taga wata ƴar ƙaramar drawer a jikin wadrope ɗin, tasa hannu ta Janyu, taji ta gam a rufe take da makulli.
Kamar knocking taji a ƙofar falo, sai ga Bahijja da hannu a ka, tace “Na shiga uku.”

Da gudu ta fito ɗakin, komai bata tsaya yi ba, kamar zata kife ta kawo falo, amma sai taji knocking ɗin shiru, tana sanɗa ta bude ƙofar, Wayam ba kowa.
Tuni ta murzawa ƙofar key, ta koma ɗakin Ahmad tana dariyar kanta a cikin zuciyarta.

Tace “Ashe tsoro ne kawai.”
Da ƙyar ta gano key ɗin wannan drawer, ta bude.

Kuddi ne gasu nan a jere, kowanne da nashi gefe.

Tun daga 200 har zuwa 1000, lashe baki Bahijja ta fara, kamar wadda ta samu sweet.

Ta ɗauke kowanne bandir ɗaya, ta kimtsa komai na ɗakin, kamar wani bai shigo ba, ta kwashe kuddinta haɗe da rufe ɗakin.

Ƙuddinta ta zuba a jaka, ta fice.
 *

Ba abinda ke tashi sai shewarsu, kamar ba Uwa da ƴa ba, Inna Luba kenan da Bahijja.

Sun zube kuddin da Bahijja ta sato a gaba, suna maida yawo.
“Wato kina jina Bahijja, kuddi fa ko ba nawa bane idan ina kallonsu, wani farin ciki ke saukar min.”

Cewar Inna, sai shinshina kuddin takeyi, gasu sababbi sai ƙamshi suke fitarwa.
Bahijja ta gyara zama tace “Ballantana wannan namu ne Inna, Halak Malak.”

Darawa sukayi gaba ɗaya, sai ƙara runguma kuɗɗin sukeyi a gabansu, kamar za’a ƙwace masu.
“Gaskiya shawarar nan naki Inna yayi, ɗari bisa ɗari.”

Bahijja ta faɗa bayan sun ɗan tsagaita da dariyar.
Sai da Inna Luba ta ɗan leƙa ƙofar ɗakin, taga ba kowa tsakar gidan, sannan ta fara magana murya ƙasa-ƙasa.

“ke nima fa haka nake yiwa Babanku, duk kiran babunshi ɗinnan, yana shiga wanka zan laluɓe aljihunsa, na ɗan yage rabona, yu wace sakaryar Mace zata zauna Miji baya bata kuddi, ita kuma ta zuba mai ido.”
Dariya suka saka, harda tafawa wannan karon, Inna ta ɗan ƙara leƙa tsakar gidan karo na biyu.
“Ba kowa fa Inna” cewar Bahijja, ganin hankalin Innarta yaƙi kwanciya.
“Ina na sani, kar ɗan tijarar nan yaji, ai kinsan halinsa da son kuɗɗin jaraba, zai iya sakina kan wannan batu, don zai ce na satar mai miliyan kuma ba ita garesa ba.”

Inna ta ƙarasa maganar tana kwaɓe baki.
Sosai Bahijja tayi dariya, tace “Ni dai a bar min tsoho haka, nawa ma zaki bashi cikin wannan ganimar?”

Da kyar Inna ta amince a bashi bandir ɗin 200 tunda shine ƙarami cikin kuddin.
Bayan sun kimtsa suka fice gidan wata mai bada taimako, basu koma gidan Hajiya tumba ba, domin Inna tace alkadarinta yayi sanyi.

*

Kuyi sorry masu karanta wannan buk, kwana biyu kun ji shiru, kunsan jiki da jini sai a slow, nayi ciwo ne, amma yanzu kam feel much better.

Via with me.

TAƁARƳA MAI BAKI BIYU 76-80

​[8/19, 9:54 AM] Mamu 🤓:
TAƁARYA MAI BAKI BIYU

Na

Mamu
®NWA
76-80
*****

Hankalin Bahijja yayi matuƙar tashi, da taji ƙaiƙayin sai ƙaruwa yakeyi, hannu ta ɗora a ka tace “Na shiga uku, ba dai infection ya kamani ba garin cushe-cushena.”

Da gudu tayi toilet, ta hada ruwan zafi, tayi tsarki.

Taji ƙaiƙayin yaɗan lafa mata, tazo ta kwanta a gado, tana tinanin wannan wani irin magani ne toh?

Ita kam dai Allah yasa kar ya janyu mata masifar nan data addabe dubban mata, ta infection.

 Can har bacci ya fara ɗibarta, kawai sai jin tayi tana soshe-soshe, zumbur ta miƙe, tayi kitchen, gishiri kaɗan ta ɗebo, ta dawo toilet, ta haɗashi da ruwan ɗumi, ta zauna cikin ruwan.
Ai da baƙin ciki ya yiwa Bahijja yawa, sai kawai ta fara hawaye, gashi dai Ahmad bai kulata ba, gashi kuma ciwo yana neman kamata, dama ya lafiyar kura take, tasha jin ance infection ba masifar da baya janyuwa.
Haka ta samu da kyar ta samu ɗan sauƙi, har bacci yayi awon gaba da ita.
 WASHEGARI…
Bayan Ahmad ya dawo sallar asuba, bai koma bacci ba, kwance yake, sai ji yake ya tashi da wani irin farin ciki a yau, wanda ya rasa na meye ne?

Ransa ƙal ya miƙe yayi wankansa, ya shirya, ya fito da shirinsa na zuwa ofis, da yake yana da Morning duty.
A falo ya zauna ya ƙwalawa Bahijja kira, shiru yaji.

Hakan yasa ya shiga ɗakinta, ba dan ransa yaso ba.

Wannan shine karo na biyu da zai shiga ɗakinta.
Kwance ya sameta, tana ta sharar baccinta, kasancewar jiya bata samu bacci sosai ba.
Sai da ya ƙare mata kallo, cike da sonta da kuma tsanarta, ƙafa yasa ya shureta.

“Kwaila!”

Ya furta da ƙarfi, ba shiri Bahijja ta miƙe zaune.
Ganin Ahmad yasa murna ta cikata, ta ɗauka maganinsu ne ya janyu ra’ayin Ahmad har cikin ɗakinta.

“Hahai. (dariya)” tayi a cikin zuciyarta.
Mur yasha sosai, ya fara magana.

“ke! a gidanku haka aka koya maki, ba zaki tashi ki haɗa min break ds safe ba, ke ba abinda kika sani sai zamba cikin aminci.”

Tsaki ya ƙara ja

“daga yau kinsan duties ɗina, Morning, Afternoon and Night, karki kuskura ki saɓa min, na lahira sai ya fiki jin daɗi.”
Kallonta ya ƙara yi, “wato ke gaki kin samu gidan hutu ko?, ga shimfiɗar alfarma, ga Ac, idan kika yi wasa sai kin koma inda kika fi wayo.”

Fuuuu ya juya ya fice daga ɗakin.

Ƴana mai jin kunyar kalaman da yayi mata, amma ya iya? Ji yake kamar yayi ta dukanta ko zai cire haushinta.

Amma sam! Baya fatar haka.
Bai ku tsaya jiran ta haɗa mai Break fast ba, ya kwashi wayoyinsa, yayi cikin gidansu.
Haushi ya cika Bahijja, har ya fice ta ko kasa motsawa, tunawa da tayi ba tayi sallar asuba ba, har to 8am, yasa ta miƙewa da sauri zuwa toilet.
*

Ko’ina sai ƙamshi ke tashi a gidan, karo yaci da ita a tsakiyar falo.

 fitowarta kenan daga ɗakinta, tayi wanka, ta shiryu cikin riga da siket ƴan kanti, irin masu riga har gwuiwa, kalar blue da fari, sunyi mata kyau.

Tayi rolling da blue pashmina.
“ina kwana  ya Ahmad.”

Ta gaidashi kanta a ƙasa, ta wuce bata jira jin amsawarshi ba.

Kallo yabi bayanta dashi, yana mai sauke ajiyar zuciya.
Dai-dai nan Abba da Umma suka fito, a tare suka haɗa baki wurin gaida iyayensu.

Hakan ya bawa kowa dariya dake cikin falon.
Zaune suke a dinning, kowa sai bawa cikinsa haƙƙinsa yake, Ahmad kam ya kasa ɗauke idanuwansa daga kan Maryam.

Cin abincinsa yakeyi, yayinda ya mai da Maryam MADUBIN DUBAWA.

Har iyayensu sai da suka fahimta.

Maryam ta lura itama, a cikin zuciyarta tace “Wallahi wannan karon Ya Ahmad zaka sha mamaki.”

Ture abincin dake gabanta tayi, ta miƙe, “Ni zan tafi Umma.”

Ta kallo Abba cike da shagwaɓa, “Yau ba zan iya driving ba Abba direba ya kaini school.”

Ta ƙarasa maganar tana turo baki.
Baki galala Ahmad ke kallonta, har ya manta a ina yake.

Shi fa Allah yayi shi da son shagwaɓa sosai.
“ƴar gidan Abba ga yayanki ya kai ki, ba sai direba ba.”
Da sauri ta kalle Abba, da tasan haka zai ce da bata yi wannan shagwaɓar ba, meye haɗinta da Ahmad??

Gashi ba wurin gardama, ba zata iya yiwa Abba garɗama ba.

 Sallama kawai tayi masu ta fice, tana gunguni a zuciyarta.
Ahmad yaga tsuntsu a sama gasasshe, jiki na ɓari ya miƙe, kamar zai kife table ɗin, Yabi bayanta.
Bayan fitarsu, Abba ya kallo Umma, dariya suka saka ta murna, tare da addu’ar Allah yasa burinsu ya cika.
*

 Bahijja tana idar da sallah, ta janyu wayarta ta kirawo innarta.

“Inna wai wani irin magani ne ƙawarki ta bani??”

Ko tsayawa gaisawa Bahijja ba tayi ba.

Inna najin haka, ta hau washe baki.

“Yar albarka hala yayi mugun aiki maganin?, ai maganin Hajiya bana shakkarsa.”

Katseta Bahijja tayi, tana kuka, ta bata labarin abinda ya faru.
Tuni Inna ta rikice, cewa take maza-maza kije asubiti a dubaki, tun abin bai zama Babba ba.

“ina shi Ahmad ɗin? Ki kirasa ya dawo ya kaiki asibiti.”

Cewar Inna da ƙsrfi, kamar zata speaker wayar.

“Ni nasan da kyar ne ya dawo, amma bari na jarraba na gani.”

Jiki a sanyaye Bahijja ta hau kiran Ahmad, amma kash wayarsa a kashe.

Kiran Inna ta ƙarayi back, bayan taga pls call me nata.

Bayan Inna ta ɗaga wayar, Bahijja tace mata “Wayarsa fa a kashe, ya zamuyi inna?bani da ko ficika a cikin gidan nan.”

Mamaki ya Cika Inna, “Amma Ahmad ɗinnan ya cika tsiya, dube irin ɓarin kuddin da yayi masu kafin aure.”

Ta faɗa a ranta, cike da jin baƙin ciki.
“Toh maza kije kiyi abinda na gaya maki ranar, kuma kizo yanzu ina jiranki.”

Da toh ta amsata, sukayi sallama, ta saka wayarta caji. 

Wanka ta shiga, wannan karon har wurin ya fara kumbura saboda ƙaikayin da yake mata.
Bayan ta fito ne, tayi inserting da cloves oil (Man kaninfari), shine fa ta ɗan ji sauƙi, ta ƙarasa shirinta.

Sannan ta ɗau hanyar zuwa aikin Inna, wanda ba na Allah bane.
HAPPY JUMA’AT TO YOU.

Allah ya sadamu da alƙhairan dake cikin wannan rana mai albarka.